1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa guiwar 'yan Bring Back Our Girls a Najeriya

July 18, 2014

A ziyarar da ta kai Najeriya Malala Yousafzai da ke fafatukar kare 'yancin ilimin yara mata ta bukaci hukumomin Abuja da su gaggauta ceto 'yan matan Chibok.

https://p.dw.com/p/1Cf53
Nigeria Kinderrechtsaktivistin Malala Yousafzai aus Pakistan in Abuja 13.07.2014
Hoto: Reuters

Bari mu fara da jaridar Die Welt wadda a wannan mako ta yi tsokaci a kan ziyarar da mai fafatukar nan 'yar kasar Pakistan Malala Yousafzai ta kai tarayyar Najeriya, don nuna goyon baya ga 'yan "Bring Back Our Girls" masu fafatukar ceto 'yan mata 'yan makarantar Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace tun a tsakiyar watan Afrilu.

Jaridar ta ce Malala wadda a ranar Litinin a birnin Abuja ta yi bikin cikarta shekaru 17 da haihuwa, wadda kuma kungiyar Taliban ta yi yunkurin hallakata a wani harbi a ka a shekarar 2012, ta kasance mai fafutukar kare 'yancin ilimin yara mata. A ranar Lahadi ta gana da iyaye da kuma wasu daga cikin 'yan matan Chibok da suka kubuta daga hannun Boko Haram, sannan a ranar Litinin ta gana da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan. Jaridar ta kara da cewa kwanaki kalilan bayan sace 'yan matan na Chibok Malala ta shiga cikin kamfen na Bring Back Our Girls sannan a ziyarce-ziryarce da ta kai kasashen duniya ta fito da batun 'yan matan fili. Fata dai inji jaridar, shi ne ziyarar ta kai ga ceto 'yan matan da ma sauran mutanen da 'yan bindigar suka yi garkuwa da su."

Fataucin kwayoyi don tallafa wa ayyukan tarzoma

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung labari ta buga game da kokarin yin sumogar muggan kwayoyi da aka boye a cikin tankin man diesel daga Somaliya.

Somalia Terror Shabaab Kämpfer tranieren bei Mogadishu
Hoto: picture-alliance/AP

Ta ce 'yan sandan yaki da safarar miyagun kwayoyi a tashar jirgin ruwan Mombasa da ke kasar Kenya sun kwace wani jirgin ruwa daga Somaliya bayan sun gano tan 1.3 na muggan kwayoyin heroin a ciki. Wani kaso na heroin din an garwaya shi da man diesel, wanda za a iya tacewa daga baya a dakunan harhada magunguna. Tun makonni biyu da suka wuce 'yan sanda suka tsare jirgin ruwa a garin Lamu da ke arewacin Kenya kafin su kai shi Mombabsa inda suka gudanar da bincike a cikinshi. A karshe dai ya tabbata cewa jirgin ruwan ya taso ne daga Pakistan sannan ya tsaya a Mogadishu. Gano muggan kwayoyin ya ba da haske ga irin hadin kan da ake samu tsakanin kungiyar al-Shabaab da kungiyoyi masu safarar miyagun kwayoyi. Da ma dai al-Shabaab na amfani da kudin cinikin miyagun kwayoyin wajen sayen makamai da kai hare-haren ta'addanci.

Bankwana da 'yar gwagwarmayar kwato 'yanci

Nadine Gordimer gestorben
Hoto: picture-alliance/dpa

A ranar Litinin kasar Afirka ta Kudu ta yi babban rashi na mashahuriyar marubuciyar kasar, farar fata 'yar gwagwarmayar kwatar 'yanci ba kawai na bakar fata ba a'a da ma sauran 'yan kasar da mulkin nuna wariyar jinsi ya shafa, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a labarin da ta buga gamae da Nadine Gordimer. Ta ce marubuciyar wadda ta rasu tana da shekaru 90 a duniya, a 1991 ta kasance mace 'yar Afirka daya tilo da ta samu kyautar marubuta adabi ta Nobel. Saboda sukar lamirin gwamnatin mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu, hukumomi sun yi ta sanya ido ga rubuce-rubucenta. A baya nan ma Nadine Gordimer ta yi ta nuna rashin jin dadinta da yadda sabbin shugabannin Afirka ta Kudu ke tafiyar da mukin kasar, musamman game da matsalar cin hanci da rashawa da ta yawaita a cikin kasar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe