1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfe na kara zafi a Scotland

Pinado Abdu WabaSeptember 16, 2014

Wuni biyu kafin zaben raba gardama, bangarorin da ke neman magoya baya dangane da 'yancin kan Scotland na kokarin jan ra'ayin al'umma

https://p.dw.com/p/1DDcs
Schottische Unabhängigkeit Referendum Bob Geldof
Hoto: Getty Images/D. Kitwood

Bangarori biyu da ke neman goyon bayan al'ummarsu kan ballewar Scotland daga Birtanniya suna nan suna cigaba da kokarin samun magoya baya wuni biyu kafin zabin raba gardamar da za su yi ranar alhamis.

Wadanda ke adawa da 'yancin kan na ganin cewa ballewa ka iya janyo musu karayar tattalin arziki, a yayinda wadanda ke goyon bayan 'yancin kan ke musu kallon matsorata.

Kodashike bayan da magoya bayan 'yancin kan suka fara samun rinjaye a kuri'ar jin ra'ayin jama'a, wadanda ke adawa na kokarin jan ra'ayin sauran mutanen da cewa idan har suka zauna ba tare da sun balle ba, gwamnati a tsakiya za ta kara musu iko.

Firaminista David Cameron da shugaban jam'iyyar Leba Ed Milliband da ma jagorar jam'iyyar Liberal demokrats Nick Clegg sun rattaba hannu kan sanarwar da ta tabbatar da hakan, wanda kuma aka wallafa a duk jaridun kasar, inda suka kara da cewa za ma su ma rika karbar harajinsu da kansu ba tare da an yi musu kutse ba, idan har suka cigaba da kasancewa kasa daya dunkulalliya