Jirgin sama ya hallaka mutane 103
February 11, 2014Talla
Wani jiragin saman sojan ƙasar Aljeriya ya yi hatsari, inda ya yi sanadiyyar fasinjoji 103. Rahotanni suka ce jirgin sanfurin C-130, ya fadi a birnin Oum El-Bouagh dake gabashin ƙasar, bisa rashin kyawun yanayi. Majiyar da ta bada sanarwar ta ce, jirgin na dauke da sojoji da iyalansu su 99 da kuma ma'aikatan jirgin guda hudu, kan ya fadi a nesan kilo mita 500 daga Algiers babban birnin ƙasar ta Aljeriya. inda kuma sanawar ta ce babu wanda ya tsira a hatsarin.
Mawallafi: Usman Shehu Usman Edita: Saleh Umar Saleh