1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jihar Adamawa tana cikin rudanin siyasa

June 19, 2014

Yunkurin tsige gwamna Nyako da mataimakinsa ya janyo shakku kan makomar siyasar jihar, inda jam'iyya da ke mulki ke zargin cewa, maganar duk bita-da-kulli ne ake yi wa gwamnantin

https://p.dw.com/p/1CMDd
Murtala Nyako
Hoto: DW/U. Shehu


A martanin ta bayan zarge-zargen almundahana da kudaden jihar wanda majalisar dokokin jihar ta yi a jiya Laraba a kan gwamna Murtala Nyako da mataimakinsa Bala James Ngilari daga mukamansu, Jam'iyyar APC da ke mulkin a jihar Adamawa ta ce duk shiri ne kawai.

APC ta ce ba mamakin hakan, idan aka yi la'akari da yadda dangantaka ta tabarbare tsakanin Shugaba Goodluck Jonathan da Gwamna Nyako, sakamakon wasikar da Nyakon ya rubuta wa gwamnonin arewacin kasar. Inda a cikin wasikar ya zargi Jonathan da haddasa husumar da ke hallaka rayuka a shiyar da ke wakana a yanzu.

Kakakin jam'iyyar Rev. Phenius Padiyo ya ce wasu zarge-zargen majalisar batutuwa ne da suka kasance shekaru bakwai da suka gabata, yana mai mamakin dago batun a yanzu da iskar siyasa ke busawa.

A 'yan watannin da suka gabata ma dai, sai da majalisar ta kada kuri'ar nuna gamsuwa da kyawun jagorancin Murtala Nyako, abin da masu nazarin siyasa a kasar ke cewa akwai aluje a cikin nadi. Sai dai jam'iyyar ta APC ba ta kare zarge-zargen da gamsassun hujjoji ba.

Nigeria Oppositionspartei APC
Hoto: DW/K. Gänsler

Mawallafi: Muntaqa Ahiwa
Edita: Usman Shehu Usman