1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Faransa za su taimaki Najeriya kan tsaro

Ubale MusaOctober 27, 2014

Kasashen biyu sun yi alkawarin taimaka wa Najeriyar ne musamman dan ganin ta gudanar da zabe mai inganci a cewar ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier da na Faransa Laurent Fabius.

https://p.dw.com/p/1Dcvm
Frank-Walter Steinmeier in Nigeria 27.10.2014
Hoto: picture-alliance/dpa/Bernd von Jutrczenka

Duk da cewar ziyarar da ke zaman ta hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu dai na zuwa ne daidai lokacin da kasar ke tunkahon gamawa da Ebola cikin kankanin lokaci, muhimman matsalolin rashin tsaro da ma zabe a cikin rudani dai na zaman muhimman batutuwan da suka dauki hankalin Frank Walter Steinmeier na kasar Jamus da kuma takwaransa na kasar Faransa Laurent Fabius da suka kammala ziyarar tasu tare da wata ganawar sirri da shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan.

Kasar ta Jamus dai a fadar Steinmeier a shirye take da nufin taimakawa kasar tarrayar Najeriyar tunkarar matsalar rashin tsaron da nufin tabbatar da samun yanayin zabe mai inganci a kasar.

“ A game da daya makiyin Boko Haram, muna goyon bayan duk wani kokari na sulhunta tsakanin bangarorin biyu da nufin tsagaita wuta da sakin yan matan da ake garkuwa da su. Ko bayan nan kuma za mu taimaka hana tserewar 'ya'yan kungiyar zuwa kasashe na makwabta, mun kuma zo da kuma wani agaji na hadin gwiwa a tsakanin Jamus da Faransa da nufin agazawa dubban wadanda rikicin ya rutsa da su. Game da satar wani bajamushe a sashen arewa maso gabas har yanzu bamu da sabon labari kan wannan”

Ko bayan batun rashin tsaron dai turawan sun kuma aiyyana shirin horar da wata tawaga ta kwarraru 200 da nufin tunkarar annoba shigen ta Ebola cikin gaggawa a nan gaba.

Frank-Walter Steinmeier in Nigeria 27.10.
Hoto: picture-alliance/dpa/Bernd von Jutrczenka

Najeriya ta ce ta yi nisa wajen tattaunawa da Boko Haram

Duk da cewar dai mahukuntan kasar ta Najeriya na ikirarin sun yi nisa a cikin tattaunawar tasu dai har ya zuwa yanzu babu alamun nasara bangaren na Abuja da a farkon fari suka ce akwai yiwuwar sakin 'yan mata 'yan makaranta na Chibok kafin daga baya su sauya amo.

Ambassada Aminu Wali dai na zaman ministan harkokin wajen kasar ta Najeriya dake karin haske ga ainihin matsayin da kasar ke ciki ga tunkarar rashin tsaron a halin yanzu.

“ To ni ban san ko akwai Faransa ba, ba a yi maganar Faransa a ciki ba, amma dai na san akwai hannun shugaban kasar Chadi ya shiga wannan magana kuma ya taimaka mun fara samun cigaba wajen tsagaita wuta da ma sako yaran nan, mu dai ba mu san wanda ya ba da labarin sako yaran nan ba a yau, amma dai ba mu ba ne, sai dai ina tabbatar muku akwai haske a harkar”

Abun jira a gani dai na zaman tasirin ziyarar da ke da tasiri ga Abujar da kuma ke kara dora girman kasar ta Najeriya a idanun turawan yamman.