1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar PDP ta shiga tsaka mai wuya

September 9, 2013

An janye jami'an tsaron wasu jiga-jigan sabuwar jam'iyyar PDP a daidai lokacin da rikici a jam'iyyar ke kara kazanta, gabanin babban zaben shekara ta 2015.

https://p.dw.com/p/19eM5
Hoto: DW/U.Haussa

Daukar matakin da ke kama hanyar yunkurin murkushe bangaren jam'iyyar PDP da ke mulkin Najeriyar biyo bayan jibge jami'an tsaro da suka mamaye ofishin da kuma janye 'yan sandan da ke kare lafiyar wasu manyan jami'an wannan banagaren ya haifar da maida martani mai zafi da ma tsoron illar da wannan ka iya haifarwa ga yanayin siyasar Najeriyar. Wannan mataki dai na zama na farko wajen aiwatar da barazana, ko ma gargadin da bangaren jam'iyyar PDP na Bamanga Tukur ya yi ga gwamnoni bakwai da ke jan daga da jam'iyyar da ke mulki wadanda suka nuna cewa ba barazana kawai suke ba, domin kuwa sun kai ga kaddamar da sabon ofishin jam'iyyar PDP da ya balle a Abuja.

Matakin yin fito na fito

Bude ofishin ya kara harzuka bangaren gwamnatin Najeriya da ya sanya daukar matakin da ya nuna zahirin kara jan layi da ma fito na fito a tsakanin bangarorin biyu, domin kuwa baya ga aikewa da ‘yan sanda da suka zagaye sabon ofishin da ke a unguwar Maitama a Abuja, an ma janye 'yan sandan da ke kula da lafiyar shugaban sabuwar jam'iyyar PDP Abubakar Kawu Baraje da na gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi, lamarin da ya harzukasu tare da bayyana cewa ba fa gudu ba ja da baya. Ambassada Ibrahim Kazaure jigo ne a bangaren sabuwar jam'iyyar PDP cewa ya yi.

Nigeria Rotimi Chibuike Amaechi in Lagos 02.09.2013
Gwamna Rotimi Chibuike Amaechi na jihar Rivers, da aka janyewa jami'an tsaro.Hoto: picture alliance/AP Photo

‘'Mu ba mu damu ba mun san wannan zai faru kuma mu PRP muka yi ba wanda zai mana wannan kama karyar, sinadarin mu muke da shi a hannunmu, kuma in mun so za mu yi amfani da shi a koma a yi abinda kundin tsarin jam'iyya ya ce a yi, bamu da wata shakka kuma ba gudu ba ja da baya, zamu tabbatar da cewa bamu bawa mutanenmu kunya ba, kuma za mu tsaya sai mun tabbatar da 'yancin mutanenmu ‘yan PDP wannan shi ne magana''.

A yayin da ake ci gaba da wannan tirka-tirka da ta sanya kwararru a fannin kimiyyar siyasar Najeriyar bayyana damuwa da ma daga dan yatsan da gamaiyar jam'iyyun adawar Najeriyar ke yi a kan wannan mataki da aka dauka, da suke ganin wuce iyaka ne, kuma ma karan tsaye ga demokradiyyar kasar. To sai dai ga mataimakin sakataren yada labarai na jamiyyar PDP na kasa Barrister Abdullahi Jalo yace matakin da jamiyyar PDP da gwamnati suka dauka an yi shi ne bisa doka.

‘'Kungiya bata zama hallattacciya ba in har bata da rijista, kuma ai ba yadda za'a yi a yi jamiyya guda biyu, PDP guda daya ce, don haka ba za'a sa ido wasu su bude wani ofishi na jamiyya guda ba, in haka ne suje su nemi rijistarsu mana. Jami'an tsaro da suka dauki wannan mataki sun yi dai, 'yan sanda aikinsu suke yi''.

Barazana ga tsarin demokradiyya

Amma ga Malam Hassan Sardauna kwarraren mai sharhi a fannin siyasa a Najeriya ya ce baya ga nuna damuwa a kan wannan lamari da ke da illa ga demokradiyyar Najeriya, akwai bukatar kamanta adalci idan aka yi la'akari da abin da ya faru a kungiyar gwamnonin Najeriya.

Rabiu Musa Kwankwaso
Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso na jihar KanoHoto: DW/T. Mösch

‘'Demokradiyya ta shiga cikin babbar barazana da ba ta taba shiga ba tun da aka sake dawo da mulkin farar hula a 1999, an yi rigima a zauren gwamnonin Najeriya gwamnonin nan sun yi zabe an samu kuri'a 19 da 16. A yau kuma sai 'ya'yan wannan kungiyar aka wayi gari sun kafa sabuwar jamiyyar PDP, sai aka je aka bude masu sabon ofishi, to akwai abin tsoro abin dubawa a kan wannan.''

Abin da ke kara daga hankula a kan rikicin jam'iyyar PDP a Najweriya dai, shine ana kokarin sulhu ne ake daukar matakai na murkushewa ga bangaren da ya balle abin da ke kara jefa shakku a kan yiwuwar gano bakin zaren da ma kaiwa ga sulhun.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Lateefa Mustapha Ja'afar / MNA

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani