1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Izra'ila ta soke tattaunawarta da Falasdinu

April 23, 2014

Izra'ila ta ce ta soke tattaunawar da aka shirya yi tsakaninta da Falasdinu a wannan Larabar domin samo hanyoyin wanzar da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

https://p.dw.com/p/1BnZa
Firaministan Izra'ila Benjamin Netanjahu da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas
Hoto: picture-alliance/dpa

Mai magana da yawun firaministan Izra'ilan Benjamin Natenjahu, Ofir Gendelman ya ce Izra'ilan ta dau wannan matakin ne saboda amincewar da Shugaba Mahmud Abbas ya yi na girka gwamnatin hadin gwiwa da kungiyar nan ta Hamas, wadda Izra'ilan ta dauka matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Kasar ta Bani Yahudu ta ce dukannin wanda ya zabi yin aiki tare da Hamas to a fayyace ta ke cewar ba ya son zaman lafiya. Da ya ke maida martani game da wannan mataki na Izra'ila, babban mai shiga tsakani a tattaunawar zaman lafiya tsakanin Izra'ila da Falasdinu Sa'eb Erakat ya ce ai tun ba yau ba Mr. Natenyahu ya katse duk wata tattaunawa tsakaninsu domin ya zabi cigaba da fadada matsugunan Yahudawa ne maimakon zaman sulhu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu