1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iyaye da yara Mata

January 22, 2009
https://p.dw.com/p/DrG5
Hoto: laif

Iyaye mata, da ‘Ya’ya mata a Afirka

An samu mace ta farko a matsayin shugabar ƙasa daga Liberia, haka zalika a shekara ta 2004 aka samu mace ‘yar Afirka da ta samu lambar yabo ta zaman lafiya ta duniya. Waɗannan abin koyi ne ga dukkan ‘ya’ya mata a Afirka.

A wasu shirye-shirye na musamman a gidan rediyo, shirin Ji Ka Ƙaru zai nuna irin matsaloli da wahalhalun da ‘ya’ya mata ke fuskanta.

‘Ya’ya mata tun suna ƙanana suke koyon aikace-aikace na gida kamar wanke-wanke, shara, girki da makamantan ayyuka da manyan mata ke yi, barin irin wannan aiki kuwa kusan za a ce har abada, sukan ji takaicin cewa ba su zuwa makaranta kamar yadda ‘yan’uwansu maza ke yi, amma su sai labari.

‘Ya’ya mata ma na da ‘yanci.

Shirin Ji Ka Ƙaru na so ya faɗakar da da al’umma cewa, ‘ya’ya mata ma na da ‘yancinsu kamar kowa, kuma su ma za su iya zama wani abu a rayuwa.

Shirin Ji Ka Ƙaru zai fito da wani shiri wanda zai faɗakar da su da ‘yan’uwansu maza. In suka saurari shirin, zai ba su damar fahimtar cewa, za su iya zama wani abu a rayuwarsu.

Yadda za a bi a samu nasara.

Shirin na Ji Ka Ƙaru, ba shiri ba ne na ji kawai, a’a har ma za a koyar da ‘ya’ya mata yadda za su iya tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum ba tare da tsangwama ba. Za a faɗakar da su ne ta hanyar wasan kwaikwayo da zai ja hankalinsu ta yadda za su amfana.

An yi shirin na Ji ka ƙaru a harsuna shidda, waɗanda suka haɗa da Ingilishi, Kiswahili, Faransanci, Hausa, Portuguese, da Amharic.

Shirin Ji Ka Ƙaru na samun gudunmuwa ne daga Ofishin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Jamus.