ISIS ta ƙwace iko da Al-Muthanna
July 9, 2014Talla
A cikin wata wasiƙa da gwamnatin Iraƙi ta aike da ita ga babban sakataran Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon tun a farkon wannan wata,ta tabbatar da cewar 'yan tawayen sun karɓe iko da cibiyar ta Al Muthanna da ke a yanki arewa maso yammancin birnin bagadaza.
Jakadin Iraƙi a Majalisar Ɗinkin Duniya Mohammed Ali Alhakim ya ce sakamakon rashin tsaro Iraƙin ba za ta ci gaba ba, da shirinta na lalata makaman masu guba har sai al'amura sun sake daidaita.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu