1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta ce yakar Siriya ya sabawa doka

September 8, 2013

Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya soki yunkurin Amurka na shiga Siriya da yaki ba da yardar Majalisar Dinkin Duniya ba, inda ya ce hakan ya sabawa doka.

https://p.dw.com/p/19dsd
iranischer Politiker und Außenminister seines Landes. Iranian diplomat Mohammad-Javad Zarif at the presidential office in Tehran, Iran, 04 August 2013, during a meeting with new Iranian President Hassan Rowhani (not seen). Zarif is said to be Rowhani's top candidate for the post of foreign minister. US-graduated Zarif has been Iranian envoy at the United Nations between 2002 and 2007. EPA/ABEDIN TAHERKENAREH
Mohammad Javad ZarifHoto: picture-alliance/dpa

Mr. Zarif ya bayyana hakan ne a wannan Lahadin yayin wata ziyara da ya ke a birnin Bagadazan kasar Iraki wadda ita ce irinta ta farko tun bayan da aka girka sabuwar gwamnati a kasar.

Wadannan kalamai da ministan na harkokin wajen na Iran ya yi dai na zuwa ne dadai lokacin da sakataren wajen Amurka John Kerry ke cigaba da yin taruka da zummar zawarcin kasashen duniya na bada goyon bayansu dangane da yakar Siriyan saboda tabbacin da Kerry din ya ce suna da shi cewar Assad ne ke da hannu wajen amfani da makamai masu guba a yakin kasar ta Iran.

Kasar Iran dai ita ce babbar aminiyar Siriya a yankin gabas ta tsakiya kuma ta sha nuna rashin amincewarta da afkawa gwamnatin Assad da yaki.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman