1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ikirarin nasara a yakin Gaza

Usman ShehuAugust 28, 2014

Bayan tsagaita wuta a yanzu bangarorin biyu ko wanne na cewa shi ya ci ribar yakin, yayinda talakawan da aka ruguzawa gidaje ke diban abinda ya saura daga gidajensu.

https://p.dw.com/p/1D32N
Palästinenser Israel Jubel in Gaza grüne Flaggen
Hoto: picture-alliance/Ibrahim Khati

Shugabannin Isra'ila da na Falasdinawa ko wannensu na yin ikirarin samun nasara a yakin da suka gwabza sama da wata guda, bayan tsagaita wuta a shekaran jiya Talata. Firaministan Isra'ila Benjamin Netenyahu ya yi gargadin cewa bazai lamunta da duk wani harin roka da zai fito a bangaren Falasdinawa, inda ma yace zai maida martani mai muni. Ana su bangaren shugabannin Hamas a Gaza sun yi ikirarin tilastawa Isra'ila ta janye. A halinda ake ciki mazauna birnin Gaza sun fara fitowa a bainal jama'a, inda wadanda ke da sauran gidajensu da ba'a rusa ba, suke komawa gidajensu. Wadanda aka ruguzawa gidajensu kuwa na ta yawo kan titi.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu