1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ikirari kan cin zabe a kasar Tunisiya

December 22, 2014

Bangaren Baji Elsibsi dan takara a zaben shugaban kasar Tunisiya, ya yi ikirarin lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, abun da janyo martanin shugaban kasar mai barin gado.

https://p.dw.com/p/1E8Qm
Hoto: picture-alliance/dpa

Da yake magana 'yan mintoci kadan bayan rufe runfunan zabe, Mohsen Marzouk daraktan yakin neman zaben Baji Elsibsi cewa ya yi bisa dukkan alamun da suke gani da kuma sakamakon da ke hannunsu, na nuni da cewa dan takararsu ne ya yi nasara a zaben. Tuni dai ya yi wani jawabi a gaban dumbun magoya bayansa, don nuna godiyarsa a garesu ganin yadda suka fito suka yi zabe. Sai dai daga nashi bangare Shugaba mai barin gado Moncef Marzouki, ya nuna adawarsa ga wannan ikirari, inda ya zargi bangaren na Elsibsi da taka ka'idojin demokradiyya ta hanyar ayyana kansa kafin sakamakon hukumar zabe.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal