1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hulda tsakanin kasashen Asiya da Afirka

Abdulrahman KabirApril 22, 2015

Hulda tsakanin kasashen Asiya da Afirka na karuwa musamman ta fannin ilmi da dubban dalibai daga Afirka ke zuwa kasashen kamar Malesiya

https://p.dw.com/p/1FCe9
Malaysia Skyline von Kuala Lumpur
Hoto: AHMAD YUSNI/AFP/Getty Images

Kasashen Malaysia da Najeria sun jima da huldodi kan fannoni da dama musamman ta bangaren ilmi. Jihar Kano tana daya daga cikin jihohin Nigeria da suka fara samun ribar horon da jami'o'in Malaysia ke baiwa ‘yan asalin jihar kan darussa daban-daban.

Dalibai sama da dubu biyu da dari shida ne Gwamnatin Jihar Kano ta tura zuwa kasashe daban-daban domin karo ilmi musamman a bangaren kimiyya da fasaha. Malaysia tana daga cikin kasashen Asiya da Jihar Kano ta tura dalibanta masu yawa saboda dalilai uku kamar yadda Sakataren Gwamnatin Kano Engineer Rabi'u Sulaiman Bichi ya bayyana.

Nigeria Bayero Universität in Kano
Hoto: Aminu Abubakar/AFP/GettyImages

‘Mai girma Gwamna ya duba kasashe da yawa wadanda ya kamata mu tura dalibanmu domin su ga abubuwa da ake a kasashen waje ta yadda idan sun dawo gida ba wai su yi karatu kawai ba a'a su kwaikwayo abubuwa wadanda za su sa kasarmu ta ci gaba. Haka kuma ana ganin Malesiya tana daga cikin kasashen da suka yi amfani da ilmi ta kyautata kasarsu. Abu na biyu kuma ita Malesiya dalibanmu za su fi saukin zuwa musamman mata saboda kasa ce wadda take kusan gaba dayanta ta Musulmai ce kuma Jihar Kano ka ga dukkanmu Musulmai ne. Abu na uku kuma shi kansa wajen al'adu muna ganin abubuwanmu kusan daya ne. Wannan zai taimakawa dalibanmu samun sauki wajen shiga cikin tsarin bincike ba tare da sun sha wata wahala ba.”

Wadannan dalilai sun kasance mabudi ga iyaye da suke da sha'awar tura ‘ya'yansu waje domin karatu. Wadanne darussa daliban Kano a Malaysia suka karu da su? Kamaluddeen Muhammad Lamido dalibi ne har yanzu da ya yaba da dangantakar ‘yan kasar da baki. Shi kuwa Saghir Jibrin Kawu ya karu ne da darasin zamantakewa da abokan karatu.

Malaysia Austausch-Studenten aus Nigeria
Musa Adamu daya daga cikin wadanda suka yi karatu a MalesiyaHoto: DW/Sani Maikatanga

Salisu Babba Usman tsohon dalibi yana begen Malesiya da abu daya da zarar wani ya yi maganar kasar, yana tunawa da yadda ake bin doka da oda. Shi kuwa Musa Adamu ya yi tsokacin ne kan ribar aiki da ya samu da wuri.