1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HRW ta zargi kasashen Afirka da take hakkin jama'a

Mohammad Nasiru AwalJanuary 29, 2015

Cikin rahoton da ta fitar Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce tarayyar Najeriya na sahun gaba na kasashen da ke fakewa da matsalar tsaro wajen muzgunawa jama'a.

https://p.dw.com/p/1ET7D
Zentralafrikanische Republik Gewalt Bangui 03.02.2014
Hoto: picture alliance/AP Photo

Kungiyar kare hakin dan Adam ta Human Rights Watch ta kaddamar da rahotonta na duniya na shekarar 2015, inda ta zargi gwamnatoci da tabka babban kuskure idan suka yi fatali da hakkin dan Adam don tinkarar manyan kalubalen tsaro. Rahoton ya kuma ba da haske ga yadda aka yi ta keta hakkin dan Adam a wasu kasashen nahiyar Afirka a shekarar 2014. Tarayyar Najeriya kuwa na daga cikin kasashen Afirka da wannan matsala ta fi kamari.

A cikin rahoton mai shafuka 656 wanda ke zama bugu na 25, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta duba yadda lamarin ya kasance a shekarar 2015 a kasashe fiye da 90, da kuma irin matakan da gwamnatoci suka dauka kan batun hakinn dan Adam a bara. Kungiyar ta ce keta hakin dan Adam ya taka muhimmiyar rawa wajen kazancewar rikice-rikicen da ake fama da su yanzu.

Nigeria Folteropfer Archiv 2013
Matasa ma ba su tsira daga cin zarafi ba a NajeriyaHoto: Amnesty International

Ga misali a tarayyar Najeriya rikicin da ake yi tsakanin sojojin gwamnati da 'ya'yan kungiyar Boko Haramm shi ne ya dabaibayen batun hakin dan Adam, inda kungiyar ta Human Rights Watch ta zargi bangarorin biyu da cin zarafi da kuma keta hakin fararen hula.

Shin mai ake sa rai gwamnati ta yi idan ta samu kanta cikin yaki da 'yan ta'adda? Babatunde Olugboji shi ne mukaddashin daraktan kula da ayyukan kungiyar ta Human Rights Watch ya yi karin haske. Ya ce: "Akwai batutuwa da dama game da rundunar sojin Najeriya, akwai rashin inganci da rashin kayan aiki da rashin da'a da kuma keta hakkin dan Adam a cikin rundunar kanta, abin da ke hana kawayenta tallafa mata. Abin da ya kamata Najeriya ta yi shi ne ta tabbatar sojojinta suna kiyaye hakin dan Adam"