1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hotunan Baga a tauraron dan Adam

Muntaqa AhiwaJanuary 15, 2015

Sabbin hotunan da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta fitar, sun nuna irin ta'adin da Boko Haram ta yi a Baga.

https://p.dw.com/p/1EKti
EINSCHRÄNKUNG Amnesty Meldung Nigeria Zerstörung durch Boko Haram
Hoto: Amnesty International/DigitalGlobe

Bisa ga dukkan alamu, alkaluman mutanen da kungiyar Boko Haram ta hallaka na iya zarta abin da mahukuntan Najeriya suka bayar na mutane 150, a hare-hare mafi muni da kungiyar ta kaddamar a garuruwan Baga da ma doron Baga dake cikin jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriyar.

Wasu hotunan tauraron dan Adam da kungiyar kare 'yancin bani Adama ta Amnesty International ta sako, sun fiddo da tabargaza mai munin gaske da kungiyar ta Boko Haram ta yi a garin Baga, inda rahotanni da ba na mahukunta ba, suka ce akalla mutane dubu biyu suka mutu, dama gidaje dubu uku da dari bakwai aka lalata.

Nigeria Baga 2013
Hoto: Pius Utomi/AFP/Getty Images

Hon Musa Bukar Kukawa shine shugaban karamar hukumar Kukawa ya sheda ta wayar tarho cewa bayanai da kungiyar ta amnesty ta fada babu shaci fadi a ciki:

"Kungiyoyin fararen hula da sauran ‘yan Najeriya sun bayyana takaici kan yadda ake neman boye bayanai kan hakikanin abinda ya faru wanda aka bayyana da cewa shi ne mafi muni tun lokacin da aka fara wannan rikici".

Wadannan hotunan dai, sun nuno daruruwan gawarwakin wadanda aka ce mazauna wuraren biyu ne da mayakan na Boko Haram suka kashe da harbin bindiga tare ma da kona wasu.

Kungiyar ta Amnesty International ta ce shaidun gani da ido, sun tabbatar cewa mayakan na Boko Haram sun kashe kananan yara masu yawa da ma wata matar da ke cikin nakuda.