1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman shigowa Turai ko ta wacce hanya

Jamila Ibrahim MaizangoApril 29, 2015

Wasu bakin haure da suka yi yunkurin shigowa Turai daga kasar Ghana na wayar da kan al'umma dangane da illar da ke tatare da wannan yunkuri.

https://p.dw.com/p/1FH9H
Shigowa Turai da hadarin mutuwa a Teku
Shigowa Turai da hadarin mutuwa a TekuHoto: picture-alliance/epa/F. Arena

Bakin hauren da suka tsira da rayukansu sun dauki wannan matakin ne ta hanyar hada kai da hukumomin kasar a dai-dai lokacin da ake fama da badakalar mutuwar bakin haure da ke bi ta barauniyar hanya ta cikin sahara da teku domin shiga Turai. Daya daga cikin wadannan mutane mai suna Eric Opoku ya bayyana cewan ya dade da burin shigowa Turan inda ya ce....

"Na kasance da burin zuwa Turai tun daga makaranta, domin mahaifan abokaina da ke Turai da suke kawo musu kayan kyale-kyale da motoci da sauransu, dan haka ne na dage sai na shiga Turai duk da cewa bani da wanda zai gayyace ni ko kuwa ya tsaya mini."

Yanke shawarar bi ta teku bayan gaza samun Visa

Opoku da ke da shekrau 35 a duniya ya ce bayan duk yunkurinsa na samun visa ya ci tura, sai kawai ya dauki damarar biyowa ta tekun Bahar Rum, sai dai ya ce akwai hadarin gaske dangane da biyowa ta barauniyar hanyar yana mai cewa...

Bakin haure da ke kokarin shigowa Turai
Bakin haure da ke kokarin shigowa TuraiHoto: picture-alliance/dpa/Italian Navy Press Office

"A gaskiya akwai hadari kuma mun sha wuya sanda muka yanke shawarar dawowa, hasali ma fitsarinmu muka rinka sha don tsananin kishiruwa."

Shi kuwa Ernest Lawey daya daga cikin bakin hauren wadanda suka yi sa´ar komawa gida cewa ya yi...

"Mun tashi ne daga garin Bawku na arewacin Ghana zuwa kasar Gabon zaune a saman motar dakon kaya, daga nan ne muka karasa zuwa Libiya, kuma sai da muka biya kudi aka nuna mana hanya."

Ayyukan ceto rayukan bakin haure a tekun Bahar Rum
Ayyukan ceto rayukan bakin haure a tekun Bahar RumHoto: picture-alliance/AP Photo/C. Montanalampo

Hada karfi waje guda domin shawo kan matsalar

Duk da samun shiga kasar Libya lami lafiya, hukumomin kasar sun cafke su suka koma da su gida. Opoku Ware ya bayyana cewa a yanzu ma yawancinsu da suka koma gida sun fi samun rayuwa mai inganci a Ghana. Hukumar kula da matasa ta Ghana ta yi wani shirin hadin gwiwa da Eric Opoku Ware da Ernest Lawey domin wayar da kan matasa ko a samu karancin bakin haure da ke zuwa sun hallaka a Tekun Bahar Rum a kokarinsu na shigowa Turai da suke yiwa kallon "Tudun mun tsira" musammanma matasa.