1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bama-bamai ya salwantar da rayuka a Kano

Nasir Salisu Zango daga KanoNovember 28, 2014

Sama da mutane 100 ne suka rasa rayukansu yayin da dama suka jikata sakamakon harin bama-bamai na kunar bakin wake da aka kai cikin babban masallacin Jumma'a na birnin Kano.

https://p.dw.com/p/1Dwop
Nigeria Anschlag 28.11.2014
Hoto: Reuters

Akalla mutane 100 ne suka rasu yayin da wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon wasu harin bama-bamai na kunar bakin wake da aka kai cikin babban masallacin Jumma'a na birnin Kano da ke jikin fadar masarautar Kano.

Bam na farko dai ya tashi ne a kusa da masallacin Jumma'a na sarkin Kano da ke cikin birni, inda wani dan kunar bakin wake ya tashi da bam a cikin wata mota. Daga bisani kuma wani bam din ya sake fashewa a barin gabas na masallacin, inda wasu 'yan kunar bakin wake da suka kutsa cikin masallacin suka tada nasu bama- baman da ke makale a jikinsu a cikin kwaryar masallacin.

Nigeria Anschlag 28.11.2014
Hoto: Reuters

Shaidun gani da ido sun bayyana cewar bayan bama-baman ma akwai wasu mutane dauke da bindigogi da suka ringa harbin mutane. Wani matashi mai suna Rabiu Dandago wanda ya tsallake rijiya da baya ya bayyana ya ce lamarin ya tayar masa da hankali. Wannnan harin bama-bamai da aka kai lokacin da ake gabatar da sallar Jumma'a ya haddasa rudani a birnin na Kano, wanda har ta kai matasa suka fusata tare da yunkurin afkawa jami'an tsaro da suka bayyana a wurin.

Sojoji sun bayyana a wurin inda su kuma mutane suka yi kokarin nuna musu fushinsu na rashin tabuka komai da mahukunta ke yi, lamarin da ya sa sojoji suka fara harbin kan mai uwa da wabi. Mata da kananan yara da tsofaffi ne wannan hari ya fi shafa. Wasu matasa dauke da makamai sun nufi yankin sabon gari inda galibi kabilu ne ke zama a yankin. Sai dai kuma kafin su karasa jami'an tsaro sun dakatar dasu. Lamarin da ya sa aka sanya dokar hana shiga da fita zuwa wannan yanki.