1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya hallaka mutane fiye da 60 a Pakistan

January 30, 2015

Wadanda suka rasu sakamakon harin da aka kai wani masallaci a kudancin Pakistan yayin sallar Juma'a na dada karuwa, inda adadin ya haura ya zuwa ga mutane 61

https://p.dw.com/p/1ETeh
Pakistan Angriff auf NATO Tanklastwagen in Hub 16.09.2013
Hoto: Reuters

A kalla mutane 50 sun rasu ne a wannan masallaci, yayin da wasu saka ida cikawa a gadon asibiti, wasu kuma da dama sun ji raunuka. Wannan dai shine hari mafi muni da wannan kasa ta fuskanta tun bayan wanda 'yan Taliban suka kai na ran 16 ga watan Disamba da ya yi sanadiyar rasuwar mutane 150 cikinsu 132 dukanninsu 'yan makaranta a garin Peshawar da ke arewa maso yammacin kasar. Wannan harin na yau an kai shi ne yayin da mutane ke tsakar sallar Jumma'a a cikin wani masallacin 'yan Shi'a da ke birnin Shikarpur, birnin da ke a nisan km a kalla 500 da birnin Karashi da ke kudancin wannan kasa ta Pakistan.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba