1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Har yanzu tsugunni bata kau ba a Afghanistan

September 1, 2014

Dan takara a zaben shugaban kasar Afganistan Abdullah Abdullah, ya yi barazanar dakatar da tattaunawar da ake kan batun kafa gwamnatin hadin kan kasa.

https://p.dw.com/p/1D4sC
Hoto: Wakil Kohsar/AFP/Getty Images

A ta bakin kakakin sa Abdullah Abdullah, yace idan har ya zuwa gobe ba'a dauki bukatun su na gudanar da sake kidayar kuri'un cikin yanayi na gaskiya ba, to ba shakka za su yi watsi da duk wani batu na tattaunawa. A cikin wani kashedi na farko dai da ya yi, Abdullah, ya janye wakillan sa daga hukumar zaben kasar, masu sa'ido kan batun sake kidayar kuri'un zaben da ya gudana a kasa, bayan da suka ce sun gano wata manakisa da ake kitsawa cikin kidayar.

Hukumar zaben kasar ta Afganistan dai, na sake kidayar kuri'u a kalla milian 8 da dubu daya na zaben da ya gudana a kasar zagaye na biyu, wanda aka yi ran 14 ga watan Yuni da ya gabata. A cewar kakakin na Abdullah Abdullah, hakurin su dai ya soma kawo karshe, dan haka duk wani sakamako da wannan haramtacciyar hukumar zaben za ta bayar, to al'umma za ta yi watsi da shi, muddin babu adalci a cikin sa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal