1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hanyar diflomasiya ce mafita a Ukraine

November 26, 2014

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta bayyana a ranar Larabannan cewa hayan daya tilo da za a iya kai wa ga nasarar shawo kan rikicin kasar Ukraine ita ce ta hanyar diflomasiya.

https://p.dw.com/p/1Dtzl
Merkel Bundestag Debatte zum Kanzleretat 26.11.2014
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

A cewar shugaba Markel duk da cewa lamarin abu ne mai wahala sannu a hanakali za a kai ga cimma masalaha ta hanyar diflomasiya. Shugabar ta bayyana haka ne a lokacin da take jawabi ga 'yan majalisa a birnin Berlin fadar gwamnatin ta Jamus.

" Halin da ake ciki a yankin Donetsk and Luhansk ya yi nisa da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla, saboda haka dole a ci gaba da kakaba takunkunkumi kan mahukuntan na Rasha, kuma ya zama dole mu zama masu hakuri da juriya dan ganin an kai ga nasarar shawo kan rikicin".

Merkel ta ce har yanzu suna kan bakan su na cewa mahukuntan na Moscow na kawo tarnaki ga shirye-shiryen Kungiyar Tarayyar Turai da kuma take dokar kasa da kasa.

Fiye da mutane 4000 ne dai suka rasu tun bayan barkewar rikicin tsakanin bangaren dakarun sojan kasar ta Ukraine da 'yan aware da ke samun goyon bayan kasar Rasha.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu