1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta dage a kan yin garkuwa da abokan gaba

Regina BrinkmannJuly 23, 2014

A sa'ilin da faɗa ke ci gaba da yin ƙamari tsakanin Isra'ila da Hamas yanzu haka Ƙungiyar Hamas na yin amfanin da wasu hanyoyin na sace sojojin Isra'ila da kuma wasu farar hula domin yin garkuwa da su.

https://p.dw.com/p/1ChBB
Israel Palästina Konflikt Unruhen
Hoto: Reuters

Rundunar Qassan ta Hamas wacce ke aikata aikin na sace jama'a ta ce a daran Litinin zuwa Talata ta sace wani sojin Isra'ila da ta ke yin garkuwa da shi, wanda ke cikon wasu tarin Yahudawan da ta riga ta sace. Ko da shi ke gwamnatin Israi'la ba ta tabbatar ba da labarin ba amma har yanzu jama'ar ƙasar na cikin ɓacin rai dangane da abin da ke faruwa na garkuwa da jama'a.

Hamas ta daɗe tana yin garkuwa da Yahudawa.

Hamas ta daɗe tana sace Yahudawa tana yin garkuwa da su tana kuma yin musanyarsu da magoya bayanta da Isra'ila ke tsare da su, a duk lokacin da aka zo yin tattaunwa. A shekarun 2006 dakarun Hamas suka sace wani sojin matashi Gilad Schalit mai kimanin shekaru 25 a sa'ilin wani farmakin da suka kai a rundunar sojin Isra'ila.

Israel Gaza Offensive 21.07.2014
Hoto: Reuters

A kan haka gwamnatin Isra'ila ta kwashe shekaru da dama tana neman a sako matashin, wanda kafin a sako shi sai da Isara'ila ta amince ta sako wasu sojojin da dama na Falasɗinu a shekarun 2011.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar