1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da gwamnatin hadakar kasar Nijar ke ciki

August 18, 2014

Shekara guda bayan kafa gwamnatin hadaka ta Jamhuriyar Nijar ana ci gaba da samun cece-kuce dangane da fannonin siyasa da na tattalin arziki da kuma na zamantakewa.

https://p.dw.com/p/1CwcU
Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou
Shugaba Mahamadou Issoufou (a dama) da Hama Amadou Shugaban majalisar dokoki (a hagu)Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

Shekara guda bayan da Shugaba Issoufou Mahamadou na Nijar ya kira 'yan siyasa da su kama domin kafa gwamnatin hadaka, matakin da a can baya ya haifar da rudani tsakanin 'yan kasar. Shin ana iya cewa hakarsa ta cimma ruwa?

Rikicin siyasar jamhuriyar ta Nijar na baya-bayan nan ya dauko asali ne tun bayan da Shugaba Issoufou Mahamadou ya bukaci a dama da su a cikin al'amuran tafiyar da kasar a watan Augustan shekarar bara ta 2013. Shekara guda bayan tayin ina aka kwana?

Hama Amadou, Parlamentspräsident in Niger
Hama Amadou a tsakiya yayin zaman majalisar dokokiHoto: DW/M. Kanta

Camarade Moumouni Habibhou mamba a hadin gwiwar jerin kungiyoyin fararen hula na CDTN cewa ya yi akwai nasara amma wasu 'yan siyasa sun nemi wargaza shirin.

To saidai Camarade Abdoulaziz Bouboucar daga hadin gwiwar CEPRASE ta malaman koyarwa ya ce babu wani hadin kan da aka samu.

Babu shakka an samu nasara ga matakin da Shugaba Issoufou Mahamadou ya dauka shi ne na tarwatsa jam'iyoyin siyasa na adawa domin cimma wani buri inji Alhaji Abdoulmoumouni Duluhu kakakin hadin gwiwar jam'iyoyin adawa na AMRN.

A lokacin da yake mayar da martani, Malam Assouman Adamou mai inkiyar Mani, da ke magana da yawun jam'iyar PNDS Tarayya mai mulki, ya zargi jam'iyyun na adawa da yunkurin yi wa gwamnati kafar angulu.

Brigi Rafini , Ministerpräsident Niger 2012
Brigi Rafini Firaministan Jamhuriyar NijarHoto: Getty Images

Wannan lamarin na zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyar ci-gaban al'umma ta kasa da kasa UNDP ko PNUD ta ba da rahoton cewa daga Jamhuriyar Nijar sai kurar mota bisa ci-gaban al'umma.

Mawallafi: Issoufou Mamane (daga Tahoua)
Edita: Suleiman Babayo