1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar matasa a arewacin Afirka

January 28, 2011

Bayan zanga-zangar da tayi sanadiyyar koran shugaban Tunisia daga kan mulki da irin ta dake gudana a Masar, suma kasashen arewacin Afrika na Libya da Algeria sun fara baiyana fargaba

https://p.dw.com/p/106rk
Zanga zanga a Aljeriya ta nuna zumunci da TunisiaHoto: DW

Ƙasar Tunesiya dai ita ce ta farko da ta gabatar da boren da ya kai ga korar wani ɗan kama-karya daga mulki. A kuma halin da ake ciki yanzu ƙasar ta samu wata tsayayyar gwamnatin riƙon ƙwarya, wadda zata shirya sahihin zaɓe na demokraɗiyya. A yanzu haka kuma guduwar neman canjin ya rutsa da ƙasar Masar duk kuwa da ƙaƙƙarfar rundunar tsaro da take da shi. Dangane da Aljeriya da Maroko kuwa, ba wanda ya san yadda lamarin zai kaya nan gaba a ƙasar Tunesiya ya zauna gaban akwatin telebijin yana mai nanata kallon yadda zanga-zangar ta fara daga Sidi Bouzid dake can ƙuriyar ƙasar ta Tunesiya. A can ne boren ya fara a tsakiyar watan desamban da ya wuce tare da mutuwar Muhammad Bouazizi. Bayan da talikin maras aikin yi ya shiga mawuyacin hali na ƙaƙa-nika-yi da rayuwarsa sai ya cunna wa kansa wuta yana ɗan shekaru 26 kacal da haifuwa. Zanga-zanga mai tsanani ta biyo bayan mutuwarsa ta kuma yi awon gaba da gwamnatin shugaba Ben Ali. An dai saurara daga Abdelwahab El-hani yana mai bayanin cewar:

Ya ce:"Muna da kashi goma sha uku cikin ɗari na marasa aikin yi. Amma lamarin ya fi tsamari a ƙuryar ƙasar, inda yawan marasa aikin yin ya kai na kashi saba'in cikin ɗari. Ba a daɗe da yaye ɗalibai dubu tamanin daga jami'o'in Tunesiya ba kuma dukkansu suna buƙatar guraben aiki. Hakan ta kasance babbar ƙalubala ga gwamnati."

Tunesien Tunis Proteste Demonstranten fordern Rücktritt der Übergangsregierung
Matasa suna neman gwamnatin wucin gadi a Tunisiya tayi murabusHoto: AP

Al'amura ne suka kai wa mutane iya wuya kuma tura ta kai bango, in ji wani ɗalibi ɗan ƙasar tunesiya. Amma abin nufi a nan ba Tunesiya ce kawai ba, har ma da sauran ƙasashen maƙobta dake yankin Maghreb. A ƙasar Maroko alal-misali kimanin kashi hamsin cikin ɗari na al'umarta matasa ne da suka gaza shekaru 25 na haifuwa, amma kuma kashi arba'in cikin ɗari daga cikinsu ba su da aikin yi, abin kuwa da ya haɗa har da matasan da aka yaye daga jami'o'in ƙasar. Kuma ko da yake ƙasar tana da sassaucin siyasa da girmama haƙƙin mata da kuma majalisar dokoki da gwamnati, amma fa ba ta da wata sahihiyar demkraɗiyya. Akwai mummunan giɓi tsakanin mawadata da 'yan rabbana ka wadata mu a ƙasar. An saurara daga Francis Ghiles daga cibiyar nazarin manufofin ƙasa da ƙasa a Barcelona yana mai bayanin cewar:

Ya ce:"Akwai dalilai game da irin wannan boren a duk fain asashen Maghreb. A Maroko masu hannu da shuni ne ke more rayuwarsu, kamar dai kaska ce a jikin dabba. Ta haka ba yadda za a yi a samu kwanciyar hankali. Ba wadata ne kadai ya kamata su rika more rayuwa ba. Muddin ba a kamanta adalci ba ko kuwa ko ba dade ko bajima talakawa zasu ta da kayar baya."

Ita ma Aljeriya ba a nesa take ba. Kasar na cikin mawuyacin hali dangane da zamantakewar jama'arta. An fuskanci asarar rayuka sakamakon zanga-zangar adawa a cikin wannan watan. A birane da dama na kasar an fuskanci arangama tsakanin masu zanga-zanga dake jifa da duwatsu da jami'an tsaro dake amfani da kulake da barkonon tsofuwa. Kuma ko da yake gwamnatin Aljeriya tayi alkawarin daukar nagartattun matakai a cikin gaggawa, amma ko shakka babu akwai wata sabuwar arangamar nan tafe. Francis Ghiles ya kara da bayani yana mai cewar:

Ya ce:"Idan har ire-iren wadannan abubuwa suna nanata faruwa, kamar dai a Aljeriya a baya-bayan nan da Marko a wasu 'yan shekarun da suka wuce ko kuma Tunesiya da Masar, to kuwa wajibi ne gwamnatocin asashen da lamarin ya shafa su koyi darasi. In kuwa ba su yi haka ba to kuwa abin da ya tafasa zai tarwatse a daidai lokacin da da na-sani ba ya da amfani."

Mawallafi: Ahmadu Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu