1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani jami'in kiwon lafiya ya kamu da cutar Ebola a Najeriya

August 4, 2014

Hukumomin kiwon lafiya sun ce wani liktan da ya yi wa ɗan Liberia nan magani mai fama da ciwon Ebola wanda ya mutu, shi ma ya kamu da cutar.

https://p.dw.com/p/1Coih
Symbolbild Ebola Westafrika
Hoto: Reuters

Ministan kiwon lafiya na ƙasar Onyebuchi Chukwu wanda ya tabbatar da labarin, ya ce an keɓe wasu kuma mutane guda 70 waɗanda suka yi cuɗanya da ɗan Liberia da ya mutu domin tanttance ko akwai wani daga cikinsu da ya kamu da cutar.

Patrick Sawyer wanda ma'aikacin gwamnati na Liberia ne wanda ya mutu a makonnin da suka gabata, ya kamu da cutar daga 'yar uwarsa kafin ya je Lagos da kuma Togo inda ya halarci wani taron ƙasashen yammancin Afirka. Wannan likta shi ne mutun na biyu da ya kamu da cutar a Najeriya wadda kawo yanzu ta kashe mutane sama da 800 a cikin ƙasashen Saliyo da Liberia da Guinea.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal