1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wadanda suka warke

Adrian Kriesch / ASJanuary 14, 2015

Ana yawan nuna musu wariya

https://p.dw.com/p/1EGjy
Liberia Ebola Überlebende
Hoto: John Moore/Getty Images

Galibi ana nuna wariya da kyama ga wadanda suka warke daga cutar Ebola. Abokan irin wadannan mutane kan kaurace musu da ma daina yin duk wata mu’amala da su sa’annan su kan kasance sun rasa aiyyukan da suke yi kafin kamuwa da cutar wanda hakan bai da kyau. Mutum kan kansace lafiyayye kamar kowa bayan ’yan kwanaki da warkewa kuma ba a iya kama cutar daga gareshi ko da dai kwayoyin cutar kan kasance a cikin maniyinsa na tsawon makonni. Wannan ne ma ya sanya ake son wadanda suka warke su rika amfani da kwaroron roba lokacin jima’i na tsawon akalla watanni uku.

Jinin wanda ya warke daga cutar Ebola kan kasance kunshe da wasu sinadarai da za su karesu daga sake kamuwa da cutar, sannan ana iya amfani da wadannan sinadaran wajen tallafawa wadanda ke dauke da cutar.

Babu amfani a nuna wariya ga wadanda suka warke daga Ebola don mutane ne da ke bukatar tallafi saboda irin matsananciyar rashin lafiyar da suka fuskanta. Kazalika wasunsu sun rasa ’yan uwansu sanadin kamuwa da cutar. Yana da kyau al’umma ta tallafa musu gwargwadon iyawa maimakon kara lalata irin yanayin da suke ciki.