1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tiktok zai kalubalanci dokar shugaba Biden

April 25, 2024

Kamfanin TikTok ya yi barazanar kalubalantar dokar da Shugaba Joe Biden na Amirka ya sanya wa hannu da ta bai wa kamfanin ByteDance mallakin kasar Chaina wa'adin watanni tara ya sayar da TikTok.

https://p.dw.com/p/4fCFg
Symbolbild TikTok USA
Hoto: Olivier Douliery/AFP

Shugaban kamfanin na sada zumunta da ake wallafa gajerun sakonnin bidiyo, Shou Zi Chew ya ce zai yi duk abun da ya kamata wajen kalubalantar sabuwar doka da ke barazanar haramta amfani da TikTok a Amurka. Kamfanin na TikTok ya ce zai dauki matakin shari'a wajen yin fito na fito da wannan doka da ke kokarin take 'yancin fadin albarkacin baki. Tun dai a lokacin da majalisar wakilan kasar ta amince da dokar kafin ta gabatar da ita ga shugaban kasar, shugaban kamfanin ya sha alwashin yin tsayin daka domin ganin hakan bai tabbata ba.

Karin Bayani: Chaina da Amurka na takaddama kan mallakar kanfanin TikTok

Shou Zi Chew shugaban kamfanin TikTok
Shou Zi Chew shugaban kamfanin TikTokHoto: Jose Luis Magana/AP/picture alliance

Shugaban kamfanin TikTok kenan Shou Zi Chew ya ce, mun ji majalisar Amurka ta mika kudurin dokar da ya samu sa hannu shugaban kasar da nufin haramta amfani da TikTok a Amurkar. Wannan na nufin mutane fiye da miliyan 170 za su daina amfani da wannan kafa wajen sada zumunta. Babu tantama wannan haramci kan TikTok haramci ne kanku da muryoyinku. 'Yan siyasa ka iya fadin hakan amma kar su rude ku. TikoTok ya bada kafa ga Amurkawa domin a gansu a kuma ji su shi ya sa ma mutane da dama suka sanya manhajar cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Muna da karfin gwiwa kuma za mu yaki 'yancinmu a gaban kotu."

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe BidenHoto: Stringer/SNA/IMAGO

Dokar dai da shugaba Biden ya sanya wa hannu za ta bai wa TikTok wa'adin watanni tara ya sayar da kamfani domin ya tashi daga mallakin kasar Chaina, kuma fadar gwamnati ta White na iya kara wa'adin kawai da kwana casa'in. 'Yan Majalisar Amurkar dai na ganin Manhajar ta TikTok barazana ce ga tsaron kasar inda suke ganin bayanan masu amfani shafin ka iya fada wa hannun gwamnatin Chaina. Sai dai sakatariyar yada labarai ta fadar White House Karine Jean-Pierre na cewa

Karin Bayani: Majalisar Wakilan Amirka ta amince da rufe TikTok

'Yan majalisa dai sun baje komai a fai-fai. Wannan ba batu ne na tursasa haramta manhajar ba ce, magana ce ta siyar wa da kuma tsaron kasar. Wannan ba damuwa ce ta Amirkawan da ke amfani da manhajar ba, damuwa ce ta juya akalar Tiktok kuma a bayyana yake karara abun da 'yan majalisa suka gabatar muka goyi baya. Muna son mu ganin sauyin wadanda suka mallaki manhajar ce. Abun da wannan sabuwar doka take nufi kenan."

Tambarin TikTok
Tambarin TikTok Hoto: Dan Kitwood/Getty Images

Ko a baya gwamnatin tsohon shugaban kasar Donald Trump ta yi yunkurin haramta amfani da manhajar a shekarar 2020. A yanzu haka dai ana ganin samun mai sayan kamfanin na TikTok ba zai zamo da sauki ba musamman da zai mallaki guda daga cikin manhaja mafi shahara a duniya. Ba lalle ne a samu wanda zai mallaki kamfanin cikin sauri ba. Idan har kamfani na TikTok bai aiwatar da abun da sabuwar dokar ta tanada ba zai fuskanci janye shi daga manhajar Apple da kuma Google App store a fadin Amirka.