1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Shugaban Portugal ya bukaci biyan diyya kan mulkin mallaka

April 28, 2024

Shugaban kasar Portugal Marcelo Rebelo de Sousa, ya bukaci gwamnatin Lisbon da ta duba yiwuwar biyan diyya ga kasashen da suka yi wa mulkin mallaka, ciki kuwa har da yafe musu basuka. Matakin da Lisbon ta ki amincewa

https://p.dw.com/p/4fGXp
Wani gunkin bayi da ke tsibirin 'abin kunya' a Dakar na kasar Senegal
Wani gunkin bayi da ke tsibirin 'abin kunya' a Dakar na kasar Senegal Hoto: picture alliance / AA

Gwamnatin Portugal ta ce ba ta shirya biyan diyya ba ga wadanda kasar ta yi wa mulkin mallaka. Hukumomin Lisbon na martani ne kan sanarwar da shugaban kasar ya fitar bisa radi na kashin kansa na bukatar biyan diyya ga kasashen, a wani mataki na yin waiwaye kan abubuwan da suka faru a lokacin mulkin mallaka tun daga karni na 15 har zuwa 19.

Karin bayani: Shekaru 230 da soke cinikin bayi 

Shugaba Sousa ya ce Portugal na son ta yaukaka dangartakarta da kasashen da ta yi wa mulkin mallaka ta kuma martaba tarihin abubuwan da suka faru tare da bayyana gaskiyar lamari domin fahimtar juna da kuma warware takaddama.

Karin bayani: Mutane 12 sun mutu a taron addini a kasar Portugal 

kasashen da Portugal ta yi sharafinta a lokacin mulkin mallaka na tsawon shekaru 500 sun hadar da  Angola da Mozambique da  Brazil da Cape Verde da Sao Tome da Timor ta Gabas da wasu yankuna na kasashen larabawa.

Portugal ta yi safarar mutane sama da milyan biyar daga nahiyar Afrika zuwa kasuwannin hada-hadar bayi da ke Turai.