1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Sabon takun saka ya barke tsakanin China da Philippines

April 30, 2024

Kasashen China da Philippines sun buda sabon babin takaddama a tekun kudancin China wanda Beijing ta bayyana a matsayin mallakinta ne.

https://p.dw.com/p/4fL4u
Südchinesisches Meer | Chinesische Küstenwache schiesst mit Wasserwerfer auf philippinisches Schiff
Hoto: Adrian Portugal/REUTERS

Kasar Philippines ta zargi jami'an tsaron gabar tekun kasar China da harbin wasu jiragen ruwanta guda biyu da igiyar ruwa tare da toshe hanyar shiga wani yanki na tekun kudancin China da kasashen biyu ke takaddama a kansa.

Karin bayani: China da Philippines na nuna wa juna dan yatsa

A cikin wata sanarwa jami'an tsaron gabar teku na Philippines sun ce rundunar tsaron China ta kafa wani shinge mai tsawon mita 380 da ya hana wa jiragen ruwan kasar damar shiga yankin da Beijing ta bayyana a matsayin mallakinta ne.

Daga nata bangare China ta tabbatar da hakan inda ta yi ikirarin cewa mataki ne na hana jiragen ruwar Philippines ratsawa yanki da ta ce yana karkashin ikonta.

Karin bayani: Tada jijiyoyin wuya tsakanin China da Philippines

A 'yan watanni baya-bayan dai takaddama tsakanin China da Philippines na daukar dumi da ba a taba ganin irinsa ba a tsawon shekaru, lamarin da ake fargabar ya dauki wani sabon salo.