1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Dokar takaita bakin haure a kasar Faransa

Abdullahi Tanko Bala
December 12, 2023

Faransa na tsara sabuwar dokar takaita kwararar bakin haure sai dai kuma za ta karbi ma'aikata 'yan ci rani da kasar ke bukata.

https://p.dw.com/p/4a4gN
Majalisar dokokin Faransa
Majalisar dokokin FaransaHoto: PASCAL ROSSIGNOL/REUTERS

An dai tattauna sabuwar dokar a Majalisar dokoki ta kasa a Faransa amma ba ta sami amincewa ba. Gwamnati ta gabatar da dokar a ce a matsayin masalaha tsakanin masu sassaucin ra'ayi da kuma masu tsattsauran ra'ayi. To amma a yanzu ga alama Paris za ta tsaurara daftarin dokar. Wannan kuwa na zuwa ne sakamakon harin da wani dan cirani daga Rasha ya kai wa wani malamin makaranta Bafaranshe wanda ya kara tada fargaba kan 'yan ta'adda daga kasashen waje.

Wani matashi dan kasar Mali Ahmada Siby dan shekaru 33 da haihuwa wanda ke zaune a Faransa tsawon shekaru biyar a yanzu ya yi tsokaci yayin wata zanga zangar jawo hankalin Faransa yana mai cewa.

Zanga zanga Faransa kan sabuwar dokar bakin haure
Zanga zanga Faransa kan sabuwar dokar bakin haureHoto: Mustafa Yalcin/Anadolu/picture alliance/dpa

" Ya ce gwamnatin Shugaba Emmanuel Macron ya mayar da mu ba komai ba, duk da cewa mu ke yin duk wasu ayyukan kaskanci a wuraren gine-gine ciki har da wuraren wasannin Olympics da za a yi a Paris a kakar badi da kuma wuraren cin abinci a matsayin 'yan shara."

Dokar dai har yanzu tana bukatar sahalewar majalisa. Sai dai kuma Majalisar dattijan Faransa wadda ke da rinjayen masu ra'ayin rikau ta tsaurara dokar a baya bayan nan. Akwai alamun sabuwar dokar za ta hanzarta matakan bayar da izinin mafaka ko akasin haka tare da takaita wa'adin daukaka kara da sanya tarnaki ga shirin hadewar iyalai da kuma takaita yiwuwar zuwa Faransa domin neman magani.  Lisa Faron jami'a ce ta kungiya mai zaman kanta, Cimade da ke taimaka wa 'yan gudun hijira da 'yan cirani.

Karin BayaniKokarin magance matsalar ‘yan gudun hijira

"Ta ce gwamnati ta yi alkawarin samar da doka mai adalci, amma kuma har yanzu wadannan sabbin dokoki babu shakka za su takaita 'yancin 'yan cirani tare da sanya matukar wahala su iya samun izinin zama a hukumance"

Majalisar dokokin Faransa
Majalisar dokokin FaransaHoto: PASCAL ROSSIGNOL/REUTERS

Yawancin 'yan siyasar Faransa dai na daukar 'yan gudun hijira a matsayin wani nauyi a kan gwamnati kamar yadda wani dan majalisar Alexis Izard ya ke cewa:-

"Ya ce a kowace shekara, muna bukatar korar bakin haure kimanin 4,000 wadanda suka aikata laifuka, kuma za a iya yin hakan da wannan sabuwar dokar"

Sai dai Herve Le Bras masanin tarihi a makarantar Ilmi mai zurfi EHESS a Faransa ya ce yana da ja kan wannan doka.

" Ya ce dokar shirme ce kawai kuma ba za ta yi wani tasiri akan yan gudun hijirar da ke shigowa a kowace shekara ba. Za dai ta bai wa yan siyasa ne kawai musamman masu tsattsauran ra'ayi damar kambama matsayinsu."

To amma ga Alain Fontaine shugaban kungiyar masu gidajen abinci a Faransa ya ce yana fatan gwamnati za ta dawo da tsarin nan na green card da ma fadada shi don bai wa 'yan cirani damar sajewa.

"Ya ce muna bukatar 'yan cirani saboda matasan mu sun fi so su yi aiki a fannonin fasaha ko kuma ayyuka da suka danganci kare muhalli. Ba sa son yin aiki mai wahala ko kadan."