1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magance cutar Ebola

Adrian Kriesch / ASJanuary 14, 2015

Gano cutar da wuri na da mahimmanci.

https://p.dw.com/p/1EGjv
Ebola in Liberia (Behandlung im Krankenhaus)
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Kamuwa da cutar Ebola ba wai ya na nufin karshen rayuwar mutum ba ne. Gano cutar da wuri kan taimaka wajen ceto rayuwar wanda ke dauke da ita duk da cewa ba a kai ga samo maganinta ba. Sai dai za a iya warkar da cutar ta hanyoyin da suka hada da rage kaifinta da magungunan rage radadin ciwo da na kashe kwayoyin cuta da kuma tsarin abinci mai gina jiki. Shan ruwa da yawa da shayi ko romo na da mutukar muhimmanci ga wanda ke dauke da cutar. Yana kuma da kyau ga mara lafiya ya kaucewa shan barasa.

Bisa al’ada a kan yi wa wanda ke dauke da cutar Ebola magani a wani waje na musamman da aka kebe. Marasa lafiya kan ji rashin dadi in suka ga jami‘an kiwon lafiya sanye da kayan kariya daga sama har kasa, to amma fa hakan ya zama wajibi a garesu don su kare kansu, domin ta haka ne kawai za su iya yi wa marasa lafiya magani.

A kan yi wa masu dauke da cutar Ebola magani da wasu sinadarai daga jinin jikin wadanda suka warke daga cutar ko kuma wasu sinadarai masu tsabta daga jinkinsa, sai dai ba a ko ina ne ake yin amfani da irin wannan tsarin ba wajen yi wa masu dauke da cutar magani. Yanzu haka dai ana cigaba da yin gwaje-gwaje da bincike don samo wasu hanyoyi na yin magani ga masu dauke da Ebola da ma samo magungunan cutar.