1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Kungiyar G7 za ta ci gaba da taimaka wa Ukraine

November 8, 2023

Kungiyar G7 ta sanar da cewar za ta ci gaba da tallafa wa Ukraine kan mamayar da Rasha ke yi mata tare kuma da hamzarta shirin sake gina kasar.

https://p.dw.com/p/4YXbj
Kungiyar G7 za ta ci gaba da taimaka wa UkraineHoto: Toshifumi Kitamura/Pool Photo via AP/picture alliance

Ministocin harkokin wajen kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya na kungiyar G7 da ke taron gudanar da taro a birnin Tokyo na kasar Japan sun sanar da cewar za su gaba da karfafa goyon baya wa Ukraine kan mamayar da Rasha ke yi mata.

Karin bayani: Taron ministocin harkokin wajen G7 zai mayar da hanakali kan rikicin Isra'ila da Hamas

Kazalika kungiyar ta G7 ta sha alwashin taka rawa wajen warware rikicin Gabas ta Tsakiya da ke kara muni tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas da ke ikon zirin Gaza na yankin Falasdinu.

Har ila yau kasashen na G7 sun bayar da tabbaci cewa za su ci gaba da kakaba takunkumai masu tsanani kan Rasha, tare kuma da hanzarta shirin sake gina Ukraine a cikin matsakaici da kuma dogon lokaci sanan kuma za su gaba da aiki don samar da hanyoyin shinfida zaman lafiya kan rikicin kasar.

Karin bayani: G7 na son daukar sabon mataki a kan Rasha

Jami'an diflomasiyyan kasashen na G7 da suka hadar da Amurka da Jamus da Japan da Faransa da Italiya da Burtaniya da kuma Kanada na sa ran fitar da sanarwar bai daya don yin kira da a tsagaita buda wuta a Gaza domin ba da damar kai kayan agaji zirin da rikicin ya daidai yau sama da wata guda.