1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun MDD ta umurnci Isra'ila ta kare fararen hula a Gaza

Zainab Mohammed Abubakar
January 26, 2024

Kotun kolin Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla wasu hakkokin da Afirka ta Kudu ke nema a shari’ar kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a Gaza suna da ma'ana.

https://p.dw.com/p/4biPH
Hoto: Piroschka van de Wouw/REUTERS

Alkalan kotun na kasa da kasa 15 sun amince da daukar matakan kare kisan kare dangi a kan Falasdinawa kana biyu suka yi adawa. 

Kotun ta ce ta amince da hakkin Falasdinawa a Gaza na samun kariya daga aikata kisan kare dangi, saboda Falasdinawa na a matsayin wata kungiya da ke bukatar kariya a karkashin yarjejeniyar kisan kare dangi.

Hukuncin na wannan Juma'a a birnin Hague da hankalin duniya ya karkata akai, bai shafi ainihin zargin da ake yi wa Isra'ila ba, na ko kisan kare dangi ya faru-ko kuma akasin haka, sai dai ya bukaci gaggauta tsagaita wuta kamar yadda Afirka ta Kudu ta nema.