1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kori sojojinta da suka hallaka jami'an agaji 7

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 5, 2024

kwamitin binciken da kasar ta kafa ne ya gano sojojin da aikata laifukan da suka sabawa tanadin rundunar sojin a fagen yaki, tare da yin rikon sakainar kashi ga bayanan da suke tattarawa

https://p.dw.com/p/4eTIK
Hoto: Ahmed Zakot/REUTERS

Rundunar sojin Isra'ila ta kori jami'anta 2 tare da ladaftar da wasu 3, bisa rawar da suka taka wajen kai harin da ya hallaka jami'an agaji 7 a Gaza, 'yan asalin kasashen waje a ranar Litinin din da ta gabata.

Karin bayani:Harin Isra'ila ya kashe jami'an agaji 7 'yan kasar waje a Gaza

Mai magana da yawun rundunar Rear Admiral Daniel Hagari, ya ce wani kwamitin binciken da kasar ta kafa ne ya gano sojojin da aikata laifukan da suka sabawa tanadin rundunar sojin a fagen yaki, tare da yin rikon sakainar kashi ga bayanan da suke tattarawa.

Karin bayani:Isra'ila ta ce bisa kuskure ta kashe jami'an agaji a Gaza

Jami'an agajin da harin na Isra'ila ya hallaka uku daga cikinsu 'yan Burtaniya ne, sai 1 daga Australia daya daga Poland, sai 'dan Amurka mai tushe daga Canada, da kuma direbansu Bafalasdine.

Dukkansu suna aiki ne a kungiyar agaji ta World Central Kitchen dake karkashin Jose Andres 'dan asalin kasar Spain.