1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta ce za a iya shafe 2024 ana yaki a Gaza

Mahmud Yaya Azare M. Ahiwa
January 2, 2024

Duk da shelar fara janye rabin sojojinta daga Zirin Gaza, wadanda suka kwashe kwanaki 85 suna samame ta kasa, rundunar sojin Isra'ila ta ce tana tsammanin rikici a Gaza zai ci gaba da gudana a tsawon shekara ta 2024.

https://p.dw.com/p/4ans1
Dakarun Isra'ila a Zirin Gaza
Dakarun Isra'ila a Zirin GazaHoto: Israel Defense Forces/picture alliance

A wani sakon sabuwar shekara, mai magana da yawun rundunar tsaron Isra'ila, Daniel Hagari ya ce an daidaita harkar tura dakarun soji don shirin tunkarar faɗa na tsawon lokaci. Ya ce za a janye wasu dakaru - musamman ma sojojin wucin gadi domin ba su damar sake tattaruwa.

A cewarsa waɗannan gyare-gyare ana yin su ne domin tabbatar da ganin an yi tsare-tsare da shirye-shirye da nufin ci gaba da yaƙi a shekara ta 2024.

Ya yi bayanin cewa wasu sojoji masu aikin wucin gadi za su bar Gaza tun a wannan mako don ba su damar sake kintsawa gabanin wasu ayyuka da ke tafe.

Mutum 21,978, akasari mata da ƙananan yara ne - aka kashe a Gaza tun daga ranar bakwai ga watan Oktoba da Hamas ta kai harin ta‘addanci a Isra‘ila, a cewar ma'aikatar lafiya da ke ƙarƙashin ikon kungiyar ta Hamas.

Ta kuma ce an jikkata mutum 56,697 a Gaza a tsawon wannan lokaci. Adadin ya haɗar da na mutum 156 da aka kashe da 246 da aka ji wa raunuka a tsawon sa'a 24 da ta gabata.