1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran na yunkurin kawo karshen yakin Yemen

March 12, 2023

Gwamnatin Iran ta bayyana cewar gyara tsamin danganta da ke tsakaninta da Saudiyya zai taimaka wajen sassanta rikcin da kasar Yemen ta shafe shekaru ta na fama da shi a siyasance.

https://p.dw.com/p/4OZa0
'Yan tawayen Huthi da ke fafatawa da gwamnati a YemenHoto: AFP

A cikin sanarwar da wakilicin Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, ya yi nuni da cewa farfado da dangantaka tsakanin gwamnatin Teheran da Riyadh zai bayar da damar sake sabunta yarjejeniyar tsagaita wuta da ma zama kan teburin tattaunawa don dinke barakar da ke damun gwamnatin hadin kai a Yemen.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ce, kasashen biyu suka amince da sake farfado da huldar diflomasiya a tsakaninsu tare da bude ofisoshin jakadancinsu bayan shafe tsawon shekaru 7 suna zaman doya da manja. Tun bayan rashin fara ga maciji da juna a shekarar 2014 ne dai gwamnatin Saudiyya ke jagorantar kawancen soja na gwamnatin Yemen yayin 'yan tawayen Houthi da ke yaki da gwamnati ke samun goyon bayan Iran.