1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hanyoyin kamuwa da na kare kai daga Ebola

Adrian Kriesch / ASJanuary 14, 2015

Sai an taba ruwan jikin mutun akan kamu da cutar

https://p.dw.com/p/1EGjt
Infografik Ebola Ansteckungswege haussa

Guda daga cikin hanyoyin da ake kamuwa da Ebola ita ce taba wani ruwa na jikin mai cutar wanda suka hada da jini da yawu da gumi da maniyi. Galibi likitoci da mutanen da ke kula da masu dauke da cutar sun fi kasancewa cikin hadarin kamuwa da ita.

Sauran hanyoyin kamuwa da Ebola sun hada da:

Yin jima’i

Jana’izar wanda cutar ta kashe, musamman ma wajen taba gawar.

Taba wani abu da mai cutar ya taba kamar mabudin kofa sanan mutum ya kai hannunsa ido ko wata kafa ta jiki.

Masu bincike sun gano cewar namun daji irinsu Jemage tamkar wani rumbu ne na Ebola. Haka ma abin ya ke ga Birrai wadanda kan yada cutar zuwa ga dan Adam din da ya yi mu’amala da su ko ya ci namansu. Ana iya kamuwa da cutar daga kananan dabbobi irinsu bera da gafiya. Wasu daga cikin wadanda aka fara ganowa da cutar sun ci naman irin wadannan dabbobi.

Mutum baya iya yadar da kwayar cutar Ebola ga sauran mutane har sai alamun kamuwa da cutar a jikinsa sun fara bayyana.

Bisa bincike da aka gudanar, jami’an kiwon lafiya sun hakkake cewar sauro baya yada kwayar cutar Ebola.

Masana kiwon lafiya sun ce hanya mafi inganci ta kare kai daga kamuwa da cutar Ebola ita ce dagewa wajen yin tsafta. Wanke hannu da ruwan da ke dauke da maganin kashe kwayoyin cuta ko sabulu musamman ma a wuraren da annobar ta bulla na iya taimakwa wajen kare kai. An sanya tankuna na ruwa mai sinadarin kashe kwayoyin cuta a Liberiya da Saliyo da kuma Gini sannan mutane sun kauracewa yin musabaha ko rungumar juna inda aka bijiro da sabbin hanyoyin gaisuwa duka dai da nufin kare kai.

Bincike ya nuna cewar safar hannu da irin takunkumi na kariya da kayan da jami‘an kiwon lafiya kan sanya ba sa hana kamuwa da cutar dari bisa dari. Su kan yi tasiri ne kawai in an yi amfani da su yadda ya dace. Kafin amfani da kayan, ana bukatar samun horo na musamman saboda cire su bayan an kusanci mai dauke da cutar na da sarkakiya da kuma hadari sosai. Sau daya kawai ya kamata a sanya kayan, kana doka ce a lalatasu da zarar an kammala amfani da su.

Domin kare kai daga kamuwa da Ebola musamman a wuraren da ta bulla za a iya bin wadannan matakai:

Kauracewa taba abubuwa da mutane

Kauracewa taba fuska

Tsabtace hannaye akai-akai

Ya kamata a gane cewar cutar Ebola za ta iya shiga jikin mutum ne kawai ta kafofin jikin da suka hada da Ido ko hanci ko baki ko dubura ko kuma wani rauni da ke jikin mutum.