1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amhara cikin dokar ta-baci a Habasha

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 4, 2023

Gwamnatin Habasha ta sanya dokar ta baci a yankin Amhara da ke zaman birni na biyu mafi girma a kasar, biyo bayan taho mu gama da aka yi tsakanin sojoji da kuma tsageru masu rike da makamai a Fano.

https://p.dw.com/p/4Un2Y
Habasha | Abiy Ahmed | Amhara
Firaministan Habasha Abiy AhmedHoto: Massimo Percossi/Ansa/ZUMA Press/IMAGO

Rikicin da ya barke dai ya kasance babbar matsalar tsaro ta farko da ta afku, tun bayan kawo karshen yakin basasar tsawon shekaru biyu a yankin Tigray na Habashan cikin watan Nuwambar bara. Gwamnatin yankin Amharan ce ta bukaci tallafin gwamnatin Tarayya, domin dawo da doka da oda. Cikin wata sanarwa da ya fitar, ofishin Firaminista Abiy Ahmed ya bayyana cewa ya zama wajibi a sanya dokar ta bacin domin zai yi wahala a shawo kan matsalar ta hanyar amfani da matakan da aka saba amfani da su.