1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: ECOWAS ta tura Goodluck Jonathan

Gazali Abdou Tasawa LMJ
July 16, 2020

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na jagorantar wani ayarin jami'an kungiyar ECOWAS da ya isa a birnin Bamako na Mali, a wani yinkuri na neman sansanta rikicin siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/3fQFj
Nigeria | Präsident Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck JonathanHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Da yake jawabi ga manema labarai bayan isarsa a birnin na Bamako, Shugaba Goodlock Jonathan ya ce yana cike da fatan samun nasara a aikin da ya kai shi: "A bisa goyon bayan al'ummar Mali, wacce na yi imani na da kyakkyawar aniyar shawo kan matsalolin kasar baki daya ba na daidaikun mutane ba, ina kyautata zaton za mu yi nasara a aikin da ya kawo mu. Matsaloli ne da ke da nasaba da zamantakewa wadanda ba mu da masaniya a kansu sosai. Amma duk da haka ina fatan za mu iya shawo kansu idan dai dukkanin bangarorin suka ba mu hadin kai da nuna dattaku."

Mali I Proteste gegen Ibrahim Boubacar Keita in Bamako
Mali ta rikiceHoto: Reuters/M. Rosier

Tun a yammacin Larabar da ta gabata ne dai, tawagar jami'an kungiyar ta ECOWAS karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan ta isa a birnin na Bamako. Tawagar dai ta kunshi ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar, wanda kasarsa ke shugabancin kungiyar a yanzu da shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar da kuma wasu kwararru a fannin dokokin tsarin mulki. Tuni dai ayarin jami'an kungiyar ta CEDEAO ya gana da Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta a fadarsa, kuma ganawar ta gudana a cikin armashi.

Fatan samun maslaha

Gwamnatin ta ce ita dai kam a shirye take ta bayar da hadin kanta ga kungiyar ta ECOWAS domin ganin warware matsalar. kamar dai yadda Boube Cisse Firaministan kasar ta Mali ya bayyana a karshen ganawar: "Da kyakkyawar aniyar shugaban kasa da ni kaina shugaban gwamnati da kuma kyakkyawan fatan da ke tattare ga kungiyar Ecowas, na yi ammanar cewa za mu shawo kan wannan rikicin siyasa domin amfanin al'ummar Mali baki daya."

A wani mataki na nuna kyakkywar aniyar ganin an shawo kan rikicin siyasar kasar, kawancen M5 na kungiyoyin da ke zanga-zangar kyamar gwamnatin ta Mali, ya sanar da dage zanga-zangar da ya yi niyyar shiryawa a Juma'ar wannan makon.

Mali Bamako Anti Regierungsproteste Imam Mahmoud Dick  Anhänger
Zanga-zangar kin jinin gwamnati a MaliHoto: Reuters/M. Rosier

Abdourahmane Diarra na Jam'iyyar URD da ke zaman mamba a kawancen na M5, ya bayyana matsayin kungiyarsa kan zuwan ayarin jami'an na ECOWAS da kuma abin da suke tsammani: "Muna farin ciki da zuwan ayarin jami'an kungiyar ECOWAS Mali, kuma a namu gani akwai batutuwa biyu zuwa uku da ya kamata jami'an su mayar da hankali kansu. Na farko a gudanar da bincike mai zaman kansa kan batun kisan masu zanga-zanga da aka yi, inda jami'an tsaro suka buda wuta kan mutanen da ba su dauke da makamai. Batu na biyu shi ne, na bukatarmu ta ganin shugaban kasa ya yi murabus domin wannan ita ce manufar kawacen M5."

Ko haka zai cimma ruwa?

Shugaba Jonathan da sauran mambobin ayarin nasa, za su ci gaba da ganawa da bangarorin da ke da ruwa da tsaki a rikicin siyasar kasar ta Mali, inda daya bayan daya zai gana da wakilan kawancen M5 mai adawa da gwamnatin IBK da jam'iyyun siyasa na bangaren masu mulki, da wakillan kungiyoyin farar hula da kuma 'yan majalisar dokokin da ake tababa kan zabensu, kafin daga karshe tawagar ta fitar da shawarwari kan hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen rikicin siyasar a Mali, wacce ke ci gaba da fuskantar hare-haren 'yan ta'adda da fadace-fadacen kabilanci. Abin jira dai a gani a nan gaba shi ne tasirin da zuwan tawagar jami'an kungiyar ta CEDEAO zai yi wajen samar da daidaito tsakanin 'yan siyasar a Mali.