1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargaba bayan faduwar jirgi marasa matuki a Nijar

Issoufou Mamane MAB
April 18, 2024

Wannan ba shi ne karon farko ba da aka samun hadarin jirgi marasa matuki a Jamhuriyar Nijar ba, amma faduwarsa a wani gida a Tahoua ya firgita al'umma duk da cewar ba a samu salwantar rai ba.

https://p.dw.com/p/4ewTh
Jami'an tsaro da sojojin kasashen waje da a jibge a Nijar a baya sun saba amfani da jirgi marasa matuki
Jami'an tsaro da sojojin kasashen waje da a jibge a Nijar a baya sun saba amfani da jirgi marasa matukiHoto: Getty Images/AFP/P. Guyot

Tun bayan da Jamhuriyar Nijar ta tsinci kanta cikin matsalar ta'adanci ne gwamnantin kasar ke daukan matakai don shawo kan lamarin tsaro  a fadin kasar ciki har da jihar Tahoua, inda sojoji ke amfani da jirage marasa matuka wajen yaki da ta'adanci musamman ma wajen tattara bayanan sirri ko kai wa 'yan bindiga hari ta sama. Sai dai kasancewar na'urar a daya daga cikin wuraren ya sa ta cin karo tare da fadowa wata unguwa ba tare da ya haddasa wata mumunar barna ba, kamar yadda mazauna unguwar da abin ya faru suka shaida wa DW.

Karin bayani: Ra'ayoyi sun bambanta kan kama makaman yaki a Niamey

Birnin Agadez na daga vikin wuraren da ke da yawan jirage marasa matuka a Nijar
Birnin Agadez na daga vikin wuraren da ke da yawan jirage marasa matuka a NijarHoto: picture-alliance/AP Photo/French Defense Ministry/M. Buis

Faduwar jirgi marasa matukin ya jefa mazauna garin Tahoua cikin damuwa inda suke kallon jiragen a matsayin wata barazana ga tsaro da rayuwarsu, kamar yadda. Malam Aliyu da ke zama daya daga cikin masu wannan fargaba ya bayyana. Mutane da dama na ganin cewar shawagin da jirage marasa matuka ke yi a sararin samaniya na zaman wata barazana ga al'umma. Sai dai Mounkaila Amadou, wani mai sharhi kan al'amuran tsaro ya ce babu wani abun shan kai da ke kawo makamancin wannan tunanin kasancewar a kowane aiki a kan samu kuskure .

Karin bayaniPistorius na neman karfafa huldar tsaro da Nijar

Mounkaila Amadou ya kara da cewar wani abin alfahari ne ga al'ummar Nijar kasancewar jiragen marasa natuka na nuna cewar gwamnantin na sa ido sosai a kantsaron lafiyar al'umma.  Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake samun hadarin makamantan wadannan jirage marasa matuka ba a Jamhuriyar Nijar, inda ko a yankin Agadez sojojin Amirka ke amfani da su, ana samun faduwarsu amman ba tare da jikkata kowa ba.