1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fararen hula na shakku kan siyasar Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou daga NiameyApril 14, 2016

Gamayyar kungiyoyin farar hulla mai suna Collectif Resistance Citoyenne ta lashi takobin yin fito na fito da nufin sake ceto tafiyar demokuradiyya a Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/1IW7H
Gebäude der Nationalversammlung in Niamey Niger
Hoto: DW

[No title]

A cikin wata sanarwa da suka fitar kungiyoyin sun caccaki yadda aka gudanar da zabubbuka da yadda aka nada gwamnatin kasar, abin da suka ce suna kira ga 'yan kasar da su fito don su jajirce.

Sanarwar sabon kawancen na kungiyoyin farar hula mai suna Resistance Citoyenne da akalla ta kai shafi uku, kumshe take da wasu bayyanai da suka shafi manyan kura-kurran da suka lura an tabka a zabubukan da aka gabatar a baya da ma yadda 'yan kungiyoyin suka kira neman yin kane-kane akan madafan iko da gwamnatin jamhuriya ta bakwai ke yi, bisa wasu dalilai da suka saba wa dokoki tafiyar da Jamhuriya.

Niger Wahl Präsident Mahamadou Issoufou gibt seine Stimme ab.
Wasu 'yan farar Hula sun zargi Issoufou da gurganta demokuradiyyaHoto: DW/A. Amadou

Kawancen ya ce tuni kasar Nijar ta fita daga tafarkin demokuradiyya ta kama wata hanya ta daban da ke neman shimfida danniya Inji Kakakinsu Malam Siradjo Issa na kungiyoyin Mojen, wanda ya ce "mun dauri aniyar kokuwa da mulkin kama karya a cikin jamhuriyar Nijar a matsayinmu na kungiyoyin fararen hula, a nunama masu mulkin nan da cewar basu da hurumin su mulki 'yan kasar Nijar saboda ba a zabesu ba,"

Kungiyoyin sun dora laifi kan gwamnatin Nijar


Wasu jamaa da ma na kurkusa ga hukumomin kolin kasar sun kasance masu sukar matsayin na 'yan fararen hular tare da cewar matsayin fafutuka ce kurum da ta zo daidai da irin ta 'yan adawa, Abubuwan da 'yan farar hullar suka ce ba a nan take ba.

Sai dai tuni aka fara samun banbancin raayi a jerin 'yan kungiyoyin farar hular na Nijar inda tuni wasu ke ganin akidar kokuwar da sabon kawancen na Collectif Resistance Citoyenne ya bullo da shi ba zai haifar wa Nijar da mai Ido ba. Ya ce " In dai su 'yan demokuradiyya ne na gaskiya ya kamata da cewar su tattara duk laifin da aka yi, suje su ajiye zuwa wani wurin da suka fi kowa sanin hanya. Anya kuwa akwai demoukuradiyyar da ke basu damar yin haka ?"

Niger Wahlen Unabhängige Wahlkommission (CENI)
kungiyoyin suka ce hukumar zabe ta CENI na da nata laifinHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo


Kungiyoyin na Resistance Citoyenne sun kuma kalubalanci matakin da ministan cikin gida na wancan lokacin ya dauka na dakatar da daya daga cikin 'yan gwagwarmayar daga hukumar zabe mai zaman kanta ta CENI bayan ya ajiye aiki , wanda suka ce hakan ya sabawa kaida.