1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin samun zaman lafiya a Najeriya

July 4, 2023

Jim kadan da kama aiki, manyan hafsoshin tsaron Najeriya sun ce za su yi duk mai yiwuwa a kokarin samar da zaman lafiya cikin kasar.

https://p.dw.com/p/4TOrF
Symbolbild Nigeria Angreifer befreien tausend Häftlinge aus Gefängnis
Jami'an 'yan sandan NajeriyaHoto: Olamikan Gbemiga/AP Photo/picture alliance

Sun dai zo a cikin babban fata, da kila kokarin cikon alkawarin masu siyasa, ga sabbabin hafsoshi na tsaron tarayyar Najeriya da ke shirin kamun aiki a cikin rudani.

Kama daga sashen arewacin kasar zuwa na kudancinsa dai, tsaron ya na shirin ya gagari kundila. Bayan kisan kudi maras adadi amma kuma ba tare da kaiwa ya zuwa ga bukata ba.

To sai dai kuma sabbabin hafsoshi na tsaron, sun ce suna shirin ciro ruwa daga dutse, da nufin burge masu takama da siyasar, da ma ragowar jama'ar garin da ke bukatar mai ceto.

Nigeria Nuhu Ribadu Präsidentschaftskandidat
Me bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Nuhu Ribadu Hoto: AP

Bayan wata ganawarsu da shugaban kasar dai, sabo na mashawarci na tsaron taraiyar Najeriyar, Malam Nuhu Ribadu dai ya ce batun zama na lafiya ko ana ha maza ha kuma mata, zai dauki hankali na jami'an tsaron kasar a halin yanzu.

Koma ta ina sabbabi na jami'an tsaron suke shirin su bi da nufin iya nasara daga in da abokan taku suka kasa dai, kururuwa ta neman sulhu dai na kara samun shiga cikin fage na siyasar tarrayar Najeriyar da nufin kare rikicin.

Tsohon gwamnan jihar ta Zamfara daya kuma a ciki na jihohin da ke ji a jiki daga rikicin masu kisa da satar shanu dai ya ce akwai bukatar sulhu da 'yan bidigar da ke yankin na Arewa maso Yamma.

Sanata Ahmed Sani Yarima dai ya ce ana bukatar sulhun da ya ce na iya kai wa ya zuwa bude sabon babi da kila ma ya kai karshen zubar jinin mazauna yankin.

Nigerianischer Soldat
Sojin NajeriyaHoto: Kim udbrook/dpa/picture-alliance

Tarrayar Najeriyar dai ta share shekara da shekaru ta na gwada kwanji, a tsakaninta da dillallan zubar jinin, amma kuma ba tare da mai da su zuwa tarihi ba.

To sai dai kuma da kamar wuya iya sulhun a cikin tsarin da ya game barayi da masu kokarin kare kai a fadar Kabiru Adamu da ke sharhi cikin batun rashin tsaron

Abun jira a gani ddai na zaman matakan yan mulkin dake fadin zama na lafiya amma kuma ba tare da fayyace hanyoyi ba.