1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Majalisa ta dage dokar zabe

Uwais Abubakar Idris LMJ
December 22, 2021

Majalisar dattawan Najeriya ta gaza yin gaban kanta a kan kin amincewa da dokar zabe da shugaban kasar ya yi, inda suka daga batun zuwa watan Janairun badi.

https://p.dw.com/p/44j7Z
Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

'Yan majalisar dattawan na Najeriya dai sun shiga da zumma da ma azamar tattaunawa a kan wannan batu da ya tayar da kura da hayaniya a tsakanin 'yan majalisar, tun bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ki sanya hannu a kan gayaran fuska da aka yi wa dokar zaben. Sanatocin dai sun shiga zaman sirri na tsawon sa a guda, kafin daukar matakin. Wannan batu na kin sanya hannu a kan gyare-gyaren da aka yi ga dokar zaben dai, ya harzuka 'yan majalisar da dama.
Sanatoci sama da 80 suka sanya hannu na amincewa su yi wa lamarin tukin  tsaye na amfani da karfin ikonsu a kan shugaban Najeriyar. Tuni dai ra'ayoyin 'yan Najeriya suka rarraba a kan wannan batu, inda kungiyoyin farar hula ke son majalisar ta dauki matakin da ya dace. A karshe dai majalisar dattawan ta amince da kasafin kudin 2022, inda ta bi sawun ta wakilai. Duka majalisun biyu dai sun tafi hutun karshen shekara sai zuwa watan Janairun badi, domin ci gaba da aikinsu na kafa dokoki da sa ido a kan bangaren zartaswa a kokarin tsawatarwa juna.

Nigeria Wahlen 2011 Bild 2
Daga cikin gyaran da aka so yi a dokar zaben, har da zaben 'yar tinke yayin fidda gwaniHoto: DW/Gänsler