1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Daga mulkin mallaka zuwa Nazi

April 11, 2024

Zamanin mulkin mallaka Turai ta mallaki wurare da samun karfin iko, amma akwai matsaloli: yadda za a halatta zalunci da ci da gumi? Masana zamantakewa da al'adu na Jamus sun mayar da rarraba mutane ta hanyar launin fata.

https://p.dw.com/p/4ed0N
Mulkin mallaka na Jamus a nahiyar Afirka
Mulkin mallaka na Jamus a nahiyar AfirkaHoto: Comic Republic

Ta yaya tashin hankali ya taimaki tsarin nuna bambancin launin fata, a kasashen da Jamus ta yiwa mulkin mallaka.

A farkon shekarun 1900, sojojin mulkin mallakar Jamus sun murkushe turjiyar a ainihin cikin kasar Tanzaniya da Kamaru da Togo da kuma Namibiya ta hanyar tashin hankali da firgici wanda ba a taba tsammani ba. Daga shekarar 1905 zuwa ta 1907, boren da aka wa lakabi da Maji-Maji da kuma abin da ya biyo baya na tsattsaurar manufar kasa a Tanzaniya sun yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu 300. Kisan kare dangi na farko a karni na 20 a Namibiya ya haddasa kisan kimanin kaso 80 cikin 100 na al'ummar OvaHerero da kaso 50 cikin 100 na al'ummar Nama.

Tsarin mulkin mallaka ya sanya Turawan mulkin mallaka da masu karfin fada a ji yin alaka a kai a kai da wadanda ba Turawa ba, hakan ya janyo akidar wariyar launin fata ta kunno kai ta hanyar nuna kaskanci da daukar salon mugunta da tsarin kimiyya.

Ta yaya Jamus ta yi kokarin hallata mulkinta ta hanyar tsarin wariyar launin fata?

Nuna wariyar launin fata da tunanin akwai bambance-bambance tsakanin mutanen da ba su yi kama da juna ba, abu ne da aka amince da shi. 

Matsalar a bayyane take, abu ne mai wahala a ce ga wani yanayi a kimiyyance da ya halatta nuna wariya. Bayan haka, ta ya za a bambance mutane daga launinsu, idan har mutane suna cudanya da juna tun asali?

A shekarar 1908 masanin zamantakewa da al'adu Eugen Fischer ya isa yankin Kudu maso Yammacin Afrika da ke karkashin mulkin mallakar Jamus, domin yin nazari kan al'ummar da ake kira Rehoboth Basters. Har yanzu wannan al'ummar na nan a Namibiya, kuma zuri'ar hadakar Turawa da kuma 'yan Afirka da ke Cape, kafin  tattaki a Arewaci zuwa tsakiyar Namibiya. Suna magana da wani karin harshen Dutch, kuma rayuwarsu ta fi kama da ta Turawa kana suna bin Addinin Kirista da wasu addinai.

Amma manufar Fischer ita ce gano wasu alamun kwayoyin halitta na gado da za su tabbatar da gadon "dabi'un launin fata" wanda za su kara taimakawa gina "tsarin wariya" a ilimin halittu. Saboda in har za ka iya tabbatar da cewa akwai bambancin launin fata a kimiyyance, to za ka iya tabbatar da irin rawar da kowa zai taka a cikin al'umma a ilimance. Ko kuma, idan ana batun mulkin mallaka, hakan na bayyana dalilin da ya sanya aka hallatawa fararen fata nuna bambanci ga bakaken fatar da ke kasansu.

Ta hanyar bincike a kan yaran kabilar Baster da auna girman kokon kansu da lura da kalar gashi da kwayar idanunsu da sauran bangarori, Fischer ya yanke hukunci cewa akwai bambancin jinsi tsakanin mutane. Ya kuma yi amannar cewa mutanen da suke da asali da ruwa biyu ko fiye, sun fi asalin 'yan Afirka kima koda yake ba su kai kimar Turawa ba. Don haka sai ya yi ta yada akidar "nuna wariyar launin fata" a tsakanin al'umma. A sakamakon haka, aka haramata duk wata alaka da ta hada fararen fata da bakaken fata a baki dayan kasashen da ke karkashin mulkin mallakar Jamus.

Ta yaya rungumar tsarin wariyar launin fata a kimiyyance da masu fada a ji suka yi, ya taimaki mulkin mallaka?

Tsarin Fischer da takwarorinsa na bambance jinsi ya samu karbuwa, a matsayin hakikanin binciken kimiyya. Hakan ya sanya samun karuwar bukatar kokon kawunan mutanen da aka kashe da kasusuwansu a kasashen Tanzaniya da Namibiya, duk a wani mataki na yin bincike kan dalilin da ya sa Turawa suka fi mutanen da ake wa mulkin mallaka daraja. 

Hakan ya yiwa ma'aikatan lafiya na Turai dadi, inda suke ganin mutanen da aka yi wa mulkin mallaka ba su da darajar da za a cire su daga wadanda za a iya gudnara da binciken magunguna a kansu da kuma matsawar da likitocin Jamus suka dinga yi wa 'yan Afrika wajen hana su haihuwa. Amma kuma wannan tsarin ya wanke su daga rashin imanin da ke tattare da shi, saboda tsarin mulkin mallaka na zalunci ya bai wa masu nazarin zamantakewa da al'adu damar amfani da gawarwakin 'yan Afrika wajen yin gwaje-gwajen kimiyya da bincike da ma sharhi.

An yi ta amfani da nazarin Eugen Fischer da shawarwarinsa kan abin da ake kira da wai "tsarkin jinsi" a Afrika, kuma an yi ta yada shi a matsayin wani tsarin kula da lafiyar al'umma.

Ta yaya binciken Fischer ya shafi akidar 'yan Nazi da suka mulki Jamus?

An ce Adolf Hitler ya karanta binciken na Fischer mai taken: "Ka'dojin Gadon dan Adam da tsaftataccen jinsi", yayin da yake kurkuku. Kuma wannan tunani a kan tsaftar jinsi da fifiko tsakanin jinsin, sun yi matukar tasiri a nasa littafin mai suna Mein Kampf

Littafin 'yan Nazi na Adolf Hitler
Littafin 'yan Nazi na Adolf HitlerHoto: Wojtek Radwanski/AFP

Tabbas binciken Fischer ya yi tasiri a dokokin Nuremburg na shakarar 1935, wadanda suka shafi nuna bambancin launin fata da kyamar Yahudawa da ya bai wa gwamnatin 'yan Nazi damar yin kawar da Yahudawa da wasu al'ummomi daga Jamus.

Ko akawai kamanceceniya tsakanin 'yan Nazi da tsarin mulkin mallaka?

 Cibiyoyi masu ilimin kan zamantakewa da al'adu da fada aji da ke da akidar nuna wariya da kuma yadda Jamus ta rinka amfani da sansanonin gwale-gwale a kasashen da suka yi wa mulkin mallaka da cin-zarafi da sauran abubuwan na tursasawa, sun sanya malaman jami'a da dama tunanin cewa cin-zarafin da Jamus ta yi a kasashen da ta yi wa mulkin mallaka ya zamo mahanga ga tsarin gwamnatin 'yan Nazi har zuwa lokacin yakin duniya na biyu. Duka tsare-tsaren biyu, sun dogara kan tashin hankali, kuma suna da alaka da akidar nuna wariyar launin fata.

Da yawa daga cikin 'yan Nazi, wadanda ke kan gaba a batun rajin daukaka darajar Jamusawa da tsaftace jinsinsu kamar Fischer sun taka rawa sosai a kasashen da Jamus ta yi wa mulkin mallaka. Ernst Rodenwaldt da ya fara aiki a matsayin likitan masu mulkin mallaka a Togo da Kamaru na daga cikin irin wadannan mutane, ya kuma dasa manufofin "tsaftace jinsi".

Ana yi masa kallon babban dan rajin nuna wariya da kuma kare akidar nan ta cewa bai kamata "tsarkaken jinsin Jamusawa" ya cakudu da wadanda suke kira da "kaskantattun mutane" ba, matsayar da daga bisani aka fadada zuwa Yahudawa da bakaken fata da Romawa da Turawan da suka fito daga yankin gabashin Turai.

Mulkin mallaka na Jamus a nahiyar Afirka
Mulkin mallaka na Jamus a nahiyar AfirkaHoto: AP

Duk da alakarsu da gwamnatin 'yan Nazi da kuma tasirinsu dangane da tsarin wariyar launi da kuma rawar da suka taka wajen yin binciken kimiyya a kan bakaken fata, har bayan yakin duniya na biyu an ci gaba da girmama Fischer da Rodenwaldt a matsayin gwarazan malaman jami'a. A cikinsu babu wanda aka tuhuma kan aikinsu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar miliyoyin mutane.

Ta yaya aka ci gaba da nuna wariyar launin fata a Namibiya, bayan ficewar Jamus?

Afrika ta Kudu ta mulki Namibiya a matsayin riko tun shekarar 1919, kuma sun assasa dokokin wariyar launin fata tun daga shekarun 1940 zuwa sama. Kokarin Fischer na haramta tarayya tsakanin launukan fata da ya asassa, ya yi tasiri a dokokin mulkin wariyar launin fata da suka haramta aure tsakanin mabambantan jinsi kamar dokar hukunta wadanda suka aikata laifin da ya danganci zina da kuma wadda ta haramta aure tsakanin mabambanta jinsi. Wadannan dokoki sun ci gaba da aiki har zuwa shekara ta 1990, lokacin da Namibiya da samun 'yancin cin gashin kai daga Afirka ta Kudu.

Baki daya dai, tsarin nazari kan jinsi ya yi kokarin halatta amfani da karfi da tashin hankali na Turawa da iyalansu a kan mutanen da sukai wa mulkin mallaka. A hannu guda kuma, bai ba da wani muhimmanci a kan batun kiwon lafiyar al'umma ba. Yayin da Turawan mulkin mallakar Jamus ba su ne farko ko kuma na karshe ba cikin Turawan mulkin mallakar da suka dabbaka wannan mummunan tasarin na nuna wariya, har kawo yanzu abubuwan da tasirin wannan tsarin da ya kaskantar da dan Adam ya haifar na ci gaba da bibiyar al'umma a Afirka da Turai.