1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

An yi gwanjon agogon zinare na attajirin jirgin Titanic

April 28, 2024

An yi gwanjon agogon zinare na fasinjan da yafi kowa kudi a cikin jirgin Titanic kuma guda daga cikin attajiran duniya. Agogon ya kasance abu mafi tsada da aka taba gwanjonsa a yayin baza Kolin kayayyakin tarihi.

https://p.dw.com/p/4fGYW
Agogon John Jacob Astor da ya mutu a jirgin Titanic
Agogon John Jacob Astor da ya mutu a jirgin TitanicHoto: Henry Aldridge & Son/PA Media/dpa

Iyalan marigayi John Jacob Astor IV sun yi gwanjon agogon akan Euro milyan 1.38 kwatankwacin Dalar Amurka milyan 1.46, wanda daga bisani wani Ba'Amurke ya sayi agogon.

Karin bayani: Mutanen da ke cikin jirgin da ya bata a teku sun mutu 

Astor ya yi nasarar kubutar da matarsa Mai dauke da juna biyu daga cikin jirgin ruwan na Titanic, kafin daga bisa ya mutu a cikin jirgin da ya yi hadari a watan Afrilun 1912 kimanin shekaru 112.

Karin bayani: Attajirai biyar sun nuste a teku 

Masu gwanjon kayan tarihin jirgin na Titanic sun ce agogon ya kasance abu mafi tsada da aka sayar daga cikin tarkacen jirgin, baya ga sarewar da aka yi amfani da ita wajen nishadantar da fasinjojin jirgin na Titanic da aka sayar akan fam milyan 1.1 a 2013.