1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

An daga turar Sweden a harabar shedikwatar NATO

March 11, 2024

Firaiministan kasar Sweden Ulf Kristersson ya ce kasarsa da a baya-bayan nan ta shiga kungiyar tsaro ta NATO za ta jaddada aiki tare da kawayenta 'ko wuya ko dadi' dangane da bukatar cimma muradun kungiyar.

https://p.dw.com/p/4dPFI
Sojoji a lokacin da suke daga tutar Sweden a harabar shedikwatar NATO a Brussels
Sojoji a lokacin da suke daga tutar Sweden a harabar shedikwatar NATO a BrusselsHoto: Kenzo Tribouillard/AFP

A wannan rana ta Litinin 11 ga watan Maris 2024, aka daga tutar kasar Sweden a harabar shedikwatar NATO, da hakan ya bude sabon babin kungiyar ta NATO da  kuma hakan ya kai mambobin kungiyar zuwa 32.

Belgien Schweden tritt der NATO bei | Zeremonie am NATO-Hauptquartier
Hoto: John Thys/AFP

Karin bayani: Sweden ta zama memba na 32 na kungiyar NATO

Wasu hotunan kamfanin dillancin labarai na AFP ya nuna Firaiministan Sweden Ulf Kristersson da Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg har ma da gimbaya mai jiran gado ta kasar Denmark Victoria na kallon yadda sojoji ke daga tutar ta Sweden a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar a birnin Brussels na kasar Belgium.

Karin bayani: Matakin karshen na shigar da Sweden cikin NATO

Sweden ta dauki matakin da ya dace kuma a lokacin da ya dace, a cewar Sakatare Janar na NATO Mr. Stoltenberg tare da Firaiministan Sweden.

Karin bayani: Finland ta jaddada kudirinta na shiga NATO

Kasashen Sweden da Finland da ke kasancewa 'yan ba ruwanmu a al'amuran da suka shafi NATO tun bayan yakin duniya na II, sun mika bukatar shiga kungiyar a watan Mayun 2022.

Belgien Schweden tritt der NATO bei | Zeremonie am NATO-Hauptquartier
Hoto: Kenzo Tribouillard/AFP