1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Cika yarjejeniya tsakanin Jamus da Namibiya

Daniel Pelz Jasko Rust/Abdourahamane Hassane/SB
March 22, 2023

Gwamnatin Tarrayar Jamus ta kudiri aniyar aiwatar da yarjejeniyar sulhu a kan kisan kiyashin da ake zarginta da yi wa ‘yan Herero da Nama na kasar Namibiya duk dama cewar ana ci gaba da yin shari'ar.

https://p.dw.com/p/4P5D0
Namibiya | Masu zanga-zanga
Zanga-zanga a NamibiyaHoto: Hitradio Namibia

Tun a karshen watan Janairu aka soma gudanar da shari'ar a gaban babbar kotun Namibiya. Alkalai na kokarin neman dakatar da shirin sulhu na Jamus. Madugun 'yan adawa na Namibiya Bernadus Swartbooi da wasu fitattun wakilan Herero da Nama suke neman a yi haka.

Karin Bayani: Jamus na adawa da sabon zama da Namibiya

Sai dai ana ganin idan wadanda suka shigar da kara sun yi haka ne da nufin yin matsin lamba ga gwamnatin Jamus da alama sun makaro saboda gwamnatin Jamus da gwamnatin Namibiya sun amince cewar ta hanyar sulhu ne kawai ake iya warware matsalar tare da cewar dole ne a fayyace wasu tambayoyi a fili ta hanyar sake tattaunawa. Sevim Dagedelen ‚‘yar majalisar dokokin Jamus Bundestag ta jam'iyyar Die Linke ta ce akwai kuskure a ciki.

Namibiya | Masu zanga-zanga
Masu zanga-zanga a NamibiyaHoto: Hitradio Namibia

Mataki da gwammnatin ta Jamus ta dauka dai na yin tattaunawar kawai da gwamnatin Namibiya ba tare da wakilan Herero da Nama ba da kuma sauran al'ummar ya janyo martani cikin fushi a Namibiya. Lifalaza Simataa jigo ne daga jam'iyyar 'yan adawa na Namibiya wanda yake gani babu wani wakilici mutanen Namibiya da ke cikin wannan yarjejeniyar.

Gwamnatin Jamus ta yi tsayin daka kan batun biyan diyya da ake ta cece-kuce da shi wadda ta ba da shawara biyan Yuro (Euro) biliyan 1.1 a tsawon  shekaru 30. Kudin dai za a gudanar da aikin raya kasa a yankunan Herero da Nama. Sai wakilan  Herero da Naman suna neman a biyasu diyya a hukumance.. Nandiuasora Mazeingo shugaban wata kungiyar da ke saka ido kan kisan kare dangin ya ce ya zama wajibi a biya kudin diyya. Masu adawa da abin da ake kira "yarjejeniyar sulhu" a yanzu suna jiran ganin hukuncin da kotu za ta yanke a Namibiya.