1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara ta halaka tsofafi a China

Yusuf BalaMay 26, 2015

Wannan gobara dai ta kone gidaje goma da ake kula da tsofafin mutane a cikinsu, inda a wasu lokutan ake samun kimanin mutane 160.

https://p.dw.com/p/1FWO7
Tote nach Feuer in chinesischem Altersheim
Hoto: Reuters

A kalla mutane 38 ne suka rasu bayan wata gobara da ta tashi a wani gidan tsofaffi a tsakiyar kasar China kamar yadda rahotannin kafafan yada labarai suka nunar a ranar Talatan nan.

A cewar kamfanin dillancin labaran kasar ta China Xinhua, akwai kuma wasu mutane shida da suka sami raunika a wannan gobara da ta tashi a birnin Pingdingshan, da ke a lardin Henan, kamfanin ya kara da cewa mutane biyu daga cikin masu raunin na cikin halin rai bakwai mutu bakwai.

A kalla gidaje goma ne suka kone inda tuni ma'aikatan agaji da na kashe gobara ke ci gaba da aikin ceto har a safiyar nan ta Talata tun cikin daren jiya Litinin kamar yadda wani da ya sheda lamarin ya fada wa kamfanin dillancin labaran na Xinhua.

Har yanzu dai babu rahotanni da ke nuna musabbain wannan gobara da ta kama a wadannan gidaje da a ke ajiye kimanin tsofaffi 160.