1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Global Media Forum 2014

April 10, 2014

Fasahar intanet ta zama tushen cudanyar kasa da kasa a fannin sadarwa da tattalin arziki da kimiyya da siyasa. Wakilai fiye da 2000 za su yi nazarin wadannan muhimman al’amura dake daukar hankali yanzu.

https://p.dw.com/p/1Bfz9

Fasahar intanet ta zama tushen cudanyar kasa da kasa a fannin sadarwa da tattalin arziki da kimiyya da siyasa. Wannan kafa tana kuma kara bude kofofi ga miliyoyin mutane yadda za su rika ba da gudummmuwarsu kan al’amuran duniya fiye ma da inda suke. Wannan zamani na digital ya bude gagarumar dama, sai dai yana tattare da hadarori. Amfani da intanet ta hanyoyin da ba su dace ba abu ne da ke daukar salo iri dabam-dabam, misali amfani da fasahar intanet domin aikata cuta, wanda kawo karshensa wani kalubale ne ga masu tsara manufofi da `yan kasuwa. Deutsche Welle tana sa ran halartar wakilai fiye da 2000 a taron wannan shekara na #link:http://www.dw.de/global-media-forum/home/s-30956:Global Media Forum#, wadanda za su yi nazarin wadannan muhimman al’amura dake daukar hankali yanzu.