1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gini ta ɗauki matakin daƙile cutar Ebola

Mouhamadou Awal BalarabeMarch 29, 2015

Gwamnatin Alpha Conde ta killace gudunmomi biyar na Gini Conakry da zummar hana yaɗuwar cutar Ebola da kuma ganin bayanta kan nan da watan Afirilu mai zuwa.

https://p.dw.com/p/1Ez5F
Ebola-Virus in Guinea
Hoto: Seyllou/AFP/Getty Images

Shugaban ƙasar Gini Alpha Conde ya ɗauki wasu sabbin matakai a fannin kiwon lafiya da nufin hana cutar Ebola yaɗuwa zuwa wasu sassa na ƙasar, a wani mataki na daƙileta kwata-kwata. A lokacin yake jawabi ta kafar talbijin a birnin Conakry Conde ya ce za a killance wasu gundumomi biyar da suka yi ƙaurin suna a sigar Ebola na tsawon kwanaki 45. Shi dai shugaban da ya sake tsayawa takara a zaɓen da zai gudana a watan Oktoba mai zuwa ya sha alwashin raba ƙasarsa da cutar ta Ebola mai saurin kisa kan nan da watan Afirilu mai zuwa.

Kasar Gini da kuma maƙwabtanta Saliyo da kuma Laberiya na ci gaba da fama da cutar Ebola shekara guda bayan ɓullarta a yankin yammacin Afirka. A ranar Jumma'a da ta gabata ma dai Ebola ta yi sanadin mutuwar wata mace a ƙasar Laberiya.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta nunar da cewar mutane 10300 Ebola ta lamashe rayukansu galibinsu a ƙasashen uku wato Gini da Saliyo da kuma Laberiya. Sannan kuma wasu ƙarin mutane 2500 sun kamu da ita.