1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin adawa da Boko Haram a Kamaru

Salissou BoukariFebruary 28, 2015

Dubun-dubatan al'ummar Kamaru sun gudanar da zanga-zanga domin nuna goyon baya ga sojojin kasar da ke fagen daga domin yakar 'yan kungiyar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1EjH1
Kamerun Präsident Paul Biya
Hoto: imago/Xinhua Afrika

Masu zanga-zangar sun ci gaba da yin Allah wadai da irin hare-haren rashin imani da 'yan kungiyar ta Boko Haram suke kaiwa a yankuna daban-daban na arewacin kasar ta Kamaru da ma na kasashe makwabta, inda suke fatan ganin an kawo karshen wannan muguwar kungiya mai tada zaune- tsaye.

Tun watanni bakwai da suka gabata ne dakarun kasar ta Kamaru ke yaki da 'yan kungiyar ta Boko Haram wadda ke rubunya kai hare-harenta ga sojoji da ma fararen hulla a yankin arewacin kasar da ke da iyaka da tarayyar Najeriya.

A halin yanzu dakarun kasar Chadi, da na Hamhuriyar Nijar sun shiga cikin wannan yaki da kungiyar ta Boko Haram da ta zame wata annoba ga wadannan kasashe. Akalla dai mutane dubu goma zuwa 15 ne suka amsa wannan kira na hadin gwiwar kungiyoyin fararan hullar kasar ta Kamaru.